Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Wata kotun daukaka kara ta mayar da Aishatu Binani a matsayin ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar APC a jihar Adamawa.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a watan Oktoba, wata babbar kotun tarayya da ke Yola, babban birnin jihar Adamawa, ta soke zaben fidda gwani na jam’iyyar APC da ya samar da Binani a matsayin dan takarar gwamnan jihar Adamawa.

Kotun ta Kuma bayyana cewar jam’iyyar APC a jihar bata da dan takarar gwamna a zaben 2023.
Kotun da mai shari’a Tanko Yusuf Hassan ya jagoranta ta yi watsi da hukuncin wata kotun tarayya da ya sauke takarar Aishatu Binani, da sanar da cewa APC ba ta da takara a zaɓen 2023.
A lokacin sanar da hukuncinsa, alkalin ya umarci a miƙa sunan Binani ga hukumar zaɓe mai zamanta wato INEC, a matsayin ‘yar takarar gwamnan APC a Adamawa.