Inganta Ilimi: Sarkin Kano ya hori daliban makarantu su rika tallafawa makarantunsu

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya nuna gamsuwarsa bisa gudumawar da tsofafin daliban Makarantar Firamaren ta Shahuchi suke bayarwa a fannin ilimi a makarantar.

 

Mai Martaba Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci makarantar domin duba wasu aiyuka da kungiyar tsofaffin dalibai sukayi na gyara wasu ajujuwa.

 

Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce mutukar tsofaffin dalibai za su rika taimakawa makarantun su hakan zai taimakawa gwamnati wajen ciyar da ilimi gaba a jihar nan dama kasa baki daya.

Talla

Cikin sanarwar da sakataren yada labaran Masarautar kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aikowa kadaura24,yace Alhaji Aminu Ado Bayero ya yabawa General Ibrahim Sani Mai ritaya sabo da gudumawar da yake bawa makarantar firamaren ta shahuchi.

Tattakin APC ya tabbatar Tinubu zai Sami kuri’a Miliyan 2 a Kano – Musa Iliyasu Kwankwaso

A nasa jawabin General Ibrahim Sani ya ce mutukar ya zama gwamnan jihar Kano a zabe shekarar 2023 zai bawa harkokin ilimi fifiko.

 

Shikuwa da yake nasa jawabin shugaban Makarantar Alhaji Umar Danbaba ya ce makarantar tana kira da gwamnatin data samar musu da jami’an tsaro da yawan malamai da dai sauran kayan aiki na zamani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...