Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa
A Najeriya, hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar ta`annati, EFCC, ta ce adadin gwamnonin da take sa-ido a kan su ya karu, wadanda take zargin suna kokarin halalta kudin haram.
A ‘yan kwanakin nan ne shugaban hukumar Abdulrasheed Bawa ya bayyana cewa wasu gwamnoni uku na shirin biyan ma’aikatansu albashi kuɗi hannu da zimmar ɓatar da sawun kuɗin sata bayan gwamnatin tarayya ta bayyana aniyarta ta sauya fasalin wasu takardun naira.
Bawa ya ce hukumar na nan a kan bakanta na lura ko sa-ido a kan jami’an gwamnati da duk wani mai take-taken halalta kudin haram, ciki har da wasu gwamnoni, wadanda suka tsara dabaru iri-iri da nufin kwashe kudin al`umma.

Shugaban hukumar EFCCn ya yi wannan bayanin ne lokacin da yake zantawa da `yan jarida a fadar shugaban Najeriya.
Ya ce sabanin adadin gwamnoni uku da hukumar ta ce tana sa-ido a kan su kimanin makwanni biyu da suka wuce, yanzu yawan irin wadannan gwamnonin ya karu. Sai dai bai fada suna ko yawansu ba.