Sojoji sun kashe yan Bindinga da yawa a wani hari da suka kai Kaduna

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Rundunar sojin saman Najeriya ta kai wani samame ta sama a kan wasu gungun ƴan bindiga da aka gano a wasu wuraren da ke cikin wasu kananan hukumomin Kaduna, inda suka kashe da dama da ga cikin su.

 

Kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, a cikin wata sanarwa da ya fitar.

 

Ya ce an yi luguden wutar a kan ƴan ta’addan ne a yankin Kawara da ke karamar hukumar Igabi a wuraren da ‘yan bindigar samu maɓoya.

 

 “An tabbatar da kashe ‘yan bindiga a harin na jirgin sama kuma wasu da aka yi garkuwa da su sun samu tserewa daga yankin gaba daya, kamar yadda wasu majiyoyi masu sahihanci na suka tabbatar.

 

“Hakazalika, a Walawa, karamar hukumar Giwa, an kai hari a wani wuri da aka yi nasarar gano wa. A karamar hukumar Chikun, an gudanar da aikin sa ido a kan Faka, Kangon Kadi, Damba, Ungwan Turai, Galbi, Gwagwada da kewaye. An ga ‘yan ta’adda a nisan kilomita 4 daga Arewa maso Yamma da Godani, kuma duk an kashe su,” inji shi.

 

Aruwan ya ci gaba da cewa a Kuduru, an ga inda ‘yan ta’addan suka kai hari da rokoki.

 

Ya ce a karamar hukumar Igabi, an gudanar da ayyuka a kan Riyawa, Alhaji Isiaka, Rima, Riyawa, Rumana, Ungwan Liman, Mai Gishiri da kuma yankin filin jirgin sama na Kaduna ba tare da sojojin sun raunata ba.

 

Ya kuma kara da cewa an samu irin wannan lamarin a Sabon Birnin, Anaba, Malumi, Wusono da Kerawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...

Da dumi-dumi: ASUU ta sanar da ranar da zata fara yajin aiki

Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci...