Daga Ibrahim Ali Muhammad
Kotun tarayya da ke zamanta a Abuja babban birnin Najeriya ta soke zaɓen fitar da gwanin gwamna na jam’iyyar APC a jihar Taraba.
Alƙalin kotun mai shari’a Obiora Egwatu ya ce la’akari da hujjoji da shaidu da aka gabatar a gaban kotu, sun nuna cewa zaɓen fitar da gwanin da ka gudanar ranar 26 ga watan Mayun wannan shekara – wanda ya ayyana Sanata Emmanuel Bwacha a matsayin ɗan takarar – ba halastacce ba ne.
A watan da ya gabata ne dai wata kotun tarayya a birnin Jalingo ta soke zaɓen fitar da gwanin da jam’iyyar ta yi wa mista Bwacha, sakamakon ƙarar da ɗaya daga cikin ‘yan takarar ya shigar a gaban kotun yana ƙalubalantar sahihancin zaɓen.

Duka kotunan biyu a hukunce-hukuncen da suka yi sun bayar da umarnin ga uwar jam’iyyar da ta sake shirya wani sabon zaɓen fitarda gwani a jihar.