Binciken ilimi da wallafe-wallafe suna da muhimmanci ga ci gaban al’umma- Dr. Zahra’u Muhd

Date:

Daga Khadija Aliyu
 Kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban jama’a ta jihar Kano, Dakta Zahra’u Muhammad Umar, ta bukaci matasa da su rika gudanar da bincike da wallafe-wallafe, domin bunkasa harkar ilimi da kuma ci gaban kansu.
 Dakta Zahra’u ta yi wannan kiran ne, lokacin da ake kaddamar da wani littafi kan adabin Larabci wanda Nasir Almalikiy Aliyyul- Khawwas Sheikh Nasir Kabara ya rubuta.
 Ta bayyana cewa, rubuta littattafai da ga matasa, zai sa su zama masu dogaro da kansu da kuma rage zaman banza a tsakanin al’umma.
Talla
 Kwamishiniyar, ta bayyana harshen Larabci a matsayin harshen da ya daukaka ilimin addinin musulunci zuwa matsayin kasa da kasa, ta hanyar bincike da kuma yiwa litattafan addini da mashahuran malaman addinin musulunci suka yi amfani da su tun a tarihi kwaskwarima.
 Dokta Zahra’u Muhammad Umar, ta yaba wa Nasir bisa jajircewarsa wajen samar da littafin, a kokarinsa na neman ilimi, inda ta ce a matsayinsa na matashi dan kasa da shekara 25, ya samu nasarar buga litattafai da dama, wadanda za su samar da ilimin da ake bukata ga dalibai.
 Ta shawarci iyaye da su rubanya kokarinsu, wajen tarbiyyantar da ya’yansu, tare da tallafa musu wajen gudanar da bincike mai ma’ana wanda zai samar da sakamako mai kyau.
 Taron ya samu halartar manyan sarakunan addini da malamai, manyan jami’an gwamnati, kafafen yada labarai da sauran jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...