Ranar ciwon Suga: Yara da yawa na kamuwa da cutar a Nigeria -Masana

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Ciwon sukari ciwo ne mai matukar hadarin gaske wanda karancin sinadarin insulin a jikin dan Adam ko gajiyar sassan jiki wajen aiki dashi ke haifarwa, ciwon sukari nada nau’i guda biyu nau’i na 1 (type one) da nau’i na 2 na ciwon sukari (type two).

Dr. Gezawa wani kwararren likitan sukari ne a asibitin koyarwa na malam Aminu kano ya bayyana cewa Kididdigar bara da gamayyar masu ciwon sukari ta duniya, (International Diabetes Federation IDF) ta fitar ta bayyana kaso daya cikin goma na mutanen dake dauke da ciwon sukari, adadinsu ya kai miliyan dari biyar da da talatin da bakwai a fadin duniya (2021), adadin da ake ganin na iya karuwa zuwa miliyan dari Bakwai da tamanin da uku Nan da shekarar 2045.
Kazalika hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cutar a matsayin cuta ta Bakwai dake yawan kashe mutane a duniya shekarar (2021) Wanda binciken ya nuna sama da kaso 50 na mutanen dake fama da ciwon sukari ba’a gano su ba a muhimmiyar ranar ta badi.
A wannan Rana hukumar ta wajabta Bada muhimmaanci ga wayar da kan jama’a game da ciwon sukari da ilimantarwa a matsayin mafita ga al’amarin cutar.
Talla
Hakan yasa gwamnatin tarayya da kungiyoyi masu zaman kansu da hadin gwaiwa da wasu kamfanoni, masu sarrafa maganin ciwon sukari sukan bada gudunmawa wurin gudanar da bikin na bana, inji Dr. Umar Isah.
 Dr. Umar Isah Umar Kwararren likitan yara ne masu ciwon sukari a asibitin koyarwa na malam Aminu, ya bayyana mana abinda ke janyo cutar, harma yace ana iya haifar yaro da ciwon sukari, ba lallai sai ya gada daga iyayen sa ba.
Dacta Umar ya  bayyana hakan ne a wurin taron wayar da kan iyayen yara, da kuma tattakin kilo Mita goma da sukayi tare da yara masu ciwon sukari a jiya Lahadi, a dakin taro na Kano club.dake Karamar hukumar Nasarawa a jihar kano.
 Wasu daga cikin yaran dake fama da ciwon sukari sun shaida wakiliyar kadaura24 ce cutar tana wahalar da su soaso idan ciwo ya tashi.
Suma dai wasu daga cikin iyayen yara sun bayyana yanda suke kula da yaransu dama irin tallafin da suke samu na allura insulin da naurar gwaji.
 Dietician Auwal Musa Shuaibu masanin cimakar Abinci ne  yayi Karin haske kan yadda masu ciwon sukari zasu daidaita cimarsu dama irin abincin Daya dace surika ci.
” Kyautuwa yayi Masu fama da irin wannan ciwo su rika yawaita cin ganyayyaki a Abincin da suke ce, bama sai Masu ciwon suga ba kowa ma yana da kyau ya rika daidaita Abincin sa don kare kansu daga kamuwa da wannan ciwo da sauran ciwuwwuka”.
Taken bikin ranar na bana shi ne (Education to Protect Tomorrow) a turance, ma’ana Ilimi domin kariyar gobe, Al muhim a wayarwa jama’a kai game da ciwon sukari domin dakile cutar nan gaba, da Kuma yadda wanda ya kamu da cutar zai rayu.
Majalisar dinkin duniya ce dai ta ware ranar 14 ga watan Nuwamba na kowacce shekara a matsayin Ranar Masu fama da ciwon suga ta duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ba zaben 2027 ne a gaba na ba – Tinubu

    Fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu...

Rikicin Masarauta: Gwamnatin Kano ta Bayyana Matsayarta Kan Hukuncin Kotu

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano kuma...

Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya tura tawaga mai karfi wajen Abba Ganduje

Daga Rahama Umar Kwaru   Babban Daraktan Hukumar Samar da Wutar...

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...