Rikicin PDP: Bani da hannu a ciki – Jonathan

Date:

 

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya musanta zargin da ake yi cewa akwai hannunsa a rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar PDP mai adawa a ƙasar.

 

Gwamnonin jiha biyar ne a yanzu ke takun-saƙa da ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar, kuma suka haƙiƙance cewa sai shugabanta na ƙasa Iyorchia Ayu ya sauka daga muƙaminsa.

 

Cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan kafofin yaɗa labarai, Ikechukwu Eze ya fitar, Jonathan ya musanta zargin da ake yi cewa da sa hannunsa a rikicin.

 

“Mun samu labari maras tushe da ake yaɗawa cewa gwamnonin da ke rikici da jam’iyya sun bayyana goyon bayansu ga Dr Goodluck Jonathan,” a cewar sanarwar. “Da mun ga dama za mu iya yin shuru da bakinmu saboda abin ba shi da wani tushe.

 

“Sai dai muna yin wannan bayani ne saboda ‘yan Najeriya da yawa sun nemi bahasi daga gare mu tare da nuna damuwa cewa za a iya kwarmata batun a jaridun ƙasa.”

 

Gwamnonin da ake yi wa laƙabi da G5 masu rigima da ɓangaren Atiku su ne: Nyesom Wike na Ribas, da Seyi Makinde na Oyo, da Okezie Ikpeazu na Abiya, da Samuel Ortom na Binuwai, da kuma Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ba zaben 2027 ne a gaba na ba – Tinubu

    Fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu...

Rikicin Masarauta: Gwamnatin Kano ta Bayyana Matsayarta Kan Hukuncin Kotu

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano kuma...

Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya tura tawaga mai karfi wajen Abba Ganduje

Daga Rahama Umar Kwaru   Babban Daraktan Hukumar Samar da Wutar...

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...