Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa
Dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin jam’iyyar ADP a zaben 2023 mai zuwa Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada, OON. ya taya tsohon zababben gwamnan jihar Kano har karo biyu Malam Ibrahim Shekarau murnar cika shekaru 67 a duniya.
Dan takarar gwamna na jam’iyyar ADP ya bayyana hakan ne a cikin wani sako da kakakin kwamitin yakin neman zabensa Abbas Yushau Yusuf ya fitar kuma ya aikowa kadaura24 a Kano.
Dan takarar Gwamna ya ce Malam Ibrahim Shekarau ya bayar da gagarumar gudunmawa a jihar Kano ta fannoni daban-daban musamman bangaren Ilimi, Inda yace al’ummar jihar kano baza su iya manta da Malam Shekarau ba.
“Tare da kudirina na inganta harkar ilimi da kuma bin manufofin jam’iyyarmu, ta ADP na inganta ilimi ta hanyar bayar da shi kyauta ga kowa da kowa kamar yadda Malam Ibrahim Shekarau ya yi fice da shi har ake kallon sa a matsayin daya daga cikin jiga-jigan da jihar Kano baza ta manta da gudunmawarsa ” Inji Sha’aban

Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada ya ce Malam Ibrahim Shekarau a matsayin sa na malamin makaranta kuma Shugaba a makarantu daban-daban a kano ya taimaka wajen ilimantar da mutane da dama a jihar kano da wasu jihohin wadanda yanzu sun zaman manya sosai da sosai.
Ya ce wadanca mutane da Malam Shekarau ya koyar da su yanzu haka da yawa daga cikinsu sun yi fice a fannoni daban-daban na rayuwa.
Dan takarar Gwamnan ya ce siyasar Malam ta da’a da mutunta jama’a ta sa ya yi suna a Kano da Najeriya da ma duniya baki daya, shi ya sa a zamanin da yake Gwamnan Jihar Kano, Jihar da al’ummarta sun samu karramawa a kowane bangare a kasar nan .
Haka kuma Sha’aban Sharada ya yaba da salon yadda Malam Shekarau ya yi mulkin sa a kano na tabbatar da shugabanci na gari wanda ya hada da bayar da ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomi wanda hakan ya taimaka wajen gudanar da aiyuka masu yawa a yankunan karkara, Inda yace Idan aka rantsar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano zai dora akan wadancan aiyuka da Malam Shekarau ya gudanar a kano.
Honorabul Sharada ya yi nuni da cewa tun farkon jamhuriya ta hudu Malam Ibrahim Shekarau ne kadai gwamnan jihar Kano da ya saki kudaden kananan hukumomi inda aka rage talauci sosai a cikin al’umma.
Sharada ya kara da cewa, da yardar Allah zai kasance Gwamna na biyu da zai ba da irin wannan cin gashin kai tare da sakin kudaden kananan hukumomi domin gudanar da ayyuka masu ma’ana ga jama’ar jihar kano baki daya.
Honorabul Sha’aban Ibrahim Sharada ya yi alkawarin dawo da martabar jihar da aka rasa idan aka zabe shi a matsayin gwamnan jihar Kano a zaben watan Maris na 2023 kuma yana fatan samun shawarwari daga Malam Ibrahim Shekarau don ciyar da kano gaba.
Dan takarar gwamna a jam’iyyar ADP ya kuma nuna rashin jin dadinsa kan yadda jihar ta rasa kima a idon mutane saboda abubawan da wannan gwamnatin ke yi.
Ya yi amfani da wannan dama a madadin iyalansa, al’ummar mazabar karamar hukumar mulki, magoya bayan jam’iyyar Action Democratic, da daukacin ‘yan kungiyar yakin neman zaben Malam domin samun lafiya, tsawon rai, da wadata.