Ganduje ya mika ta’aziyyarsa bisa rasuwar tsohon dan bal din Kano Pillars Bello K/mata

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Gwamnan jihar kano Abdullahi Umar Ganduje ya mika ta’aziyyarsa bisa rasuwar tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars Bello Musa Kofar Mata, wanda ya rasu kwanan nan. Wanda ya rasu yana da shekaru 34 a duniya.

 

Gwamna Ganduje ya mika sakon ta’aziyyar ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa Malam Abba Anwar ya fitar kuma ya aikowa kadaura24.

Talla

 

Yayin da yake addu’ar Allah ya jikan dan wasan wanda ya fara wasan kwallon kafa a Buffalo FC Kano, Kano Pillars FC, Heartland FC of Owerri, FC Ifeanyi Uba na Nnewi da Elkanemi Warriors na Maiduguri, ya mika sakon ta’aziyya ga kungiyar da kuma dangin marigayin.

 

Ya ce ya kadu Sosai da samu labarin rasuwar,Inda yayi fatan Allah ya jikansa da rahama, yace rashin Bellon babban rashi ne ga daukacin Masu harkokin kwallon kafa a Kano da kasa baki daya.

 

Ganduje ya kara da cewa, a madadin gwamnati da na al’ummar jihar Kano, yana mika sakon ta’aziyyarsa da addu’o’i na musamman ga Allah madaukakin sarki ya gafarta masa yasa aljanna ta zamo makomarsa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...