Daga Rukayya Abdullahi Maida
Majalisar dokokin jihar ta yi Allah wadai da halin rashin da’a na shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai ta tarayya, Hon Alasan Ado Doguwa kan abin da ya faru tsakaninsa da mataimakin dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar APC, Hon. Murtala Sule Garo, wanda hakan ya sabawa mutuntaka da mutuncin jam’iyyar APC.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban masu rinjaye na majalisar, Hon. Labaran Abdul Madari ya fitar, inda ya nuna cewa wannan abu da Doguwa yayi na iya kawo cikas ga ci gaban jam’iyyar a Kano.

Kadaura24 ta rawaito sanarwar ta kuma yi kira ga uwar jam’iyyar APC ta jihar kano da ta kasa baki daya da su dauki matakin da ya dace a kan Hon Alasan Ado Doguwa, duba da munanan dabi’unsa wadanda suka wuce gona da iri .
Sanarwar ta kuma bayyana cewa wannan rashin da’a ba irin Hon Murtala Sule Garo kadai aka yiwa ba, har da tsohon Sakataren Gwamnatin Jiha, Engr. Rabi’u Sulaiman Bichi, Hon. Engr. Muhd Ali Wudil, dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Garko/Wudil a majalisar tarayya da kuma kakakin jam’iyyar APC na jiha Hon Ahmed Aruwa.
Majalisar ta kuma jaddada matsayin ta na tabbatar da nasarar jam’iyyar APC mai mulki a dukkan matakai a zabe mai zuwa, in ji sanarwar ta kara da cewa.