Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Jam’iyyar APC a jihar Kano ta zargi ‘ya’yan jam’iyyar adawa ta NNPP Kwankwasiyya da yin amfani da wata ‘yar rashin jituwa a jam’iyyar APC mai mulki domin kara haifar da rashin jituwa.
Ya ce yayin da dattawan jam’iyyar suka sasanta rikicin cikin ruwan sanyi, ‘yan Kwankwasiyya da ke tsorata da karfin jam’iyyar APC a jihar suna ta yada farfaganda don zafafa lamarin.
Sanarwar gargadin ga ‘ya’yan jam’iyyar APC ta fito ne ta wata sanarwa da kwamishinan yada labarai kuma kakakin yakin neman zaben Gawuna/Garo Com. Muhd Garba a ranar Alhamis.

Ya ce akwai sahihan bayanai da ke nuna cewa kungiyar Kwankwasiyya har ta kai ga lalata fastocin yan APC , kuma ta yin hakan ne domin sake rura wutar rikicin da ake kokarin shawo kana ta.
Malam Garba ya yi nuni da cewa a ‘yan kwanakin da suka gabata ‘yan Kwankwasiyya sun yi ta watsa hotuna tare da ba su ma’ana mara kyau a kokarinsu na bata sunan jam’iyya mai mulki a jihar.
Kwamishinan ya ci gaba da cewa, rashin jituwa ya zama ruwan dare a dukkan jam’iyyu, bai kamata a bar ‘yan adawa su yi amfani da su wajen kara haifar da fitina ga jam’iyyar ba.
Ya ce a daidai lokacin da al’ummar kasar nan ke tunkarar shekarar zabe, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, suna son ‘ya’yan jam’iyyar su tsaya tsayin daka tare da tabbatar da hadin kan ta don ci gaba da tafiya a kan turbar da ake ganin za ta samu nasara a dukkan matakai.