Daga Isa Ahmad Getso
Alkalin kotun majistiri mai lamba ta 24 dake zamanta a gyadi-gyadi a jihar Kano ya umurci ofishin mataimakin sufeto janar na ‘yan sanda shiyya ta daya da ya gudanar da sahihin bincike kan laifin cin zarafin wani dan jarida da ake zargin dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Doguwa/Tudun Wada na tarayya Alhassan Ado Doguwa ya yi.
Kadaura24 ta ruwaito cewa umarnin ya biyo bayan korafin da wakilin jaridar Leadership na jihar Kano, Abdullahi Yakubu ya kai gaban kotu ta hannun lauyansa, Bashir, Umar & Co.

A cikin wasikar da aka aike wa AIG Zone One mai kwanan wata 1 ga Nuwamba, 2022, mai dauke da sa hannun magatakardar Kotun, wadda Kadaura24 ta sami kwafinta ta ce, “Babbar Kotun Majistare Mai lamba ta 24, A.B. Wali Complex, Gyedi-Gyedi Kano, domin ya rubuto tare da neman ku gudanar da bincike na gaskiya akan dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Doguwa/Tudun Wada, Alhassan Ado Doguwa.
“Bayan shigar da kara kai tsaye gaban kotu ta hannun lauyan wanda ya shigar da karar, Bashir, Umar da Co. Malam Abdullahi Yakubu dake zaune a Sharada quarters. Yace takardar tana haɗe da kwafinne na ƙarar,” in ji wasiƙar.
Sai dai a wasikar karar da lauyan wanda ya shigar da karar ya aikewa kotu ya ce, “Muna aiki ne a matsayin lauya ga Malam Abdullahi Yakubu na Sharada Quarters Kano Municipal (wanda ake kira Client dinmu) ya umarce mu nema masa hakkin sa da rubuta wannan koken sa.
A Takaitacce dai wanda muke yiwa aiki kwararren dan jarida ne da yake aiki da Jaridar Leadership anan Kano Kuma shi ne mai rikon mukamin Shugaban kamfanin dake nan Kano.
“A ranar 1 ga Nuwamba, 2022, abokin aikinmu tare da wasu kwararrun abokan aikinsa sun je gidan dan majalisar wakilan bisa gayyatar da ya yi musu saboda ya wanke kansa daga zargin ya jiwa Dan takarar Mataimakin gwamnan jihar kano a jam’iyyar APC Hon. Murtala Sule Garo rauni kamar yadda labarin yake ta yawo a kafafen sada zumunta na Zamani.