Daga Shehu Sulaiman Sharfadi
Gidauniyar Malam Ibrahim Khalil dake jihar Kano ta sha alwashin bada gudunmowar data dace domin samar da shugabanni nagari a zabukan shekara ta 2023 dake tafe.
Shugabar gidauniyar a kano Malama Bilkisu idris Adam ce ta tabbatar da hakan a lokacin da gidauniyar ta shirya taron addu’o’in dangane da tafiyar siyasar malam Ibrahim khalil wanda ya gudana a nan kano.
Malama Bilkisu tace makasudin kafa wannan gidauniyar shi ne domin wayar da kan al’umma maza da mata mahimmancin shugabanci nagari musamman a wannan lokaci da al’umma suke cikin tsananin bukatar Shugabanni nagari.

Bilkisu tace kungiyar ta shirya wannan lacca ne domin wayar da kan mata akan zabar shugaba adali kuma nagari wanda zai kawo cigaba da tallafawa alumma ta fannoni da dama.
” Lokaci yayi da mata ya kamata suyi karatun ta nutsu wajen sanin wane shugaba yakamata su zaba, domin ganin an samu kyakkkyawan sauyi a cikin rayuwar al’umma, ya kamata mata suji tsoron Allah domin Allah sai ya tambayesu a ranar gobe kiyama game da was suka zaba domin mu ne mukafi fitowa don mu yi zabe” . Inji Malam Bilkisu
Ajawabinsa Malami a jami’ar Bayero dake Kano Dr. Ahmed Saidu Dukawa ya ce shugabanci abune da yake da muhimmanci wanda shi ne yake kawo daidaito da zaman lafiya da sanin mahimmancin dan Adam, wanda yayi dogon jawabi akan shugabanci da mahimmancin siyasa a rayuwar al’umma.
Dukawa Ya shawarci yan kungiyar da suka shirya wannan taro da su kara zage damtse wajen Adana kuri’unsu, Wanda da sune zasu samu damar kawo sauyin shugaban da suke tunanin zai yi musu adalci.
A nata bangaren mai masaukin baki a yayin gudanar da taron uwar gidan Dan takarar Gwamna a jamiyyar ADC Hajiya Farida Ibrahim Khalil ta nuna matukar farin Cikinta bisa gudunmowa da addu’o’in da Gidauniyar take yiwa Malam Ibrahim khalil domin ganin an kawo sauyin shugabanci nagari a fadin jihar Kano.
Daga karshe tayi Klkira ga Gidauniyar da ta cigaba da wayar da kan al’umma musamman mata wajen sanin wa ya kamata su zaba domin ya zama shugabansu.