Yan adaidaita sahu zasu daina bin wasu hanyoyi a kano – Ganduje

Date:

Daga Aisha Aliyu Umar

 

Gwamnatin jihar kano tace ta kashe sama da Naira Miliyan Dubu biyu wajen sayo manyan Motocin safa-safa da kanana na taxi kimanin guda 150 domin Kara inganta harkokin sufuri a birnin kano.

 

Kadaura24 ta rawaito Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan lokacin da ya jagoranci kaddamar da motocin a filin wasa na Kano pillars stadium dake Sabon gari a kano, a yau lahadi.

 

Gwamna Ganduje yace an Samar da motocin ne da hadin gwiwar gwamnati da wasu yan kasuwa domin inganta harkokin sufuri a birnin Kano da Kuma magance kalubalen tsaro da ake samu da ma rage cinkoson ababen hawa a jihar.

 

” Duk birnin da ya ci gaba dole ne a inganta tare da zamanatar da harkokin sufuri a garin don haka muka Samar da wadannan motoci manya na safa-safa guda 100 da Kuma na taxi guda 50 domin Kano tayi gogayya da manyan burane a duniya kamar yadda na dade Ina fada”. Inji Ganduje

 

Talla

” Muna fata idan wadannan motoci suka fara aiki gadan-gadan, babura Masu kafa uku wadanda akafi sani da adaidaita sahu zasu koma lunguna suna aiki fito da mutane bakin hanya Inda Kuma so taxi din zasu rika fito da mutane zuwa Inda zasu hau manyan Motocin na zamani da muka samar masu cin akalla mutane 80″. Ganduje ta bayyana

 

Gwamna Ganduje yace a kokarin su na ganin ba’a tagayyara masu sana’ar tuka adaidaita sahu ba, sun samar da tsarin da za’a rika baiwa masu adaidaita sahun tukin motocin domin ganin suma an inganta Rayuwar su .

Wasu daga cikin motocin Masu lakabin kanawa Texi

Yace Motocin na safa-safa zasu rika aiki ne kowacce rana daga karfe 6 na safe zuwa 10 na dare, sanann kashin farko na Motocin zasu rika zirgar-zirga ne daga Jogana zuwa yankura, sai Kuma daga janguza zuwa Yankura sai Kuma Katsina Road zuwa Hadeja Road a kullum.

Ya bukaci al’ummar jihar kano zasu bada hadin kai domin dorewar tsarin, sannan yayi kira ga direbobin da zasu tuka motocin da su gudanar da aikinsu cikin gaskiya da amana domin al’umma su dade suna morar Sabon tsarin, wanda yace zai cigaba Inda yayi alkawarin karo motoci 200 a cikin sabuwar shekara.

 

Da yake nasa jawabin shugaban riko na cibiyar ciniki kasuwanci masana’antu ma’adanai ta harkokin noma ta jihar kano Alhaji Ahmad Aminu yace Idan motocin suka fara aiki al’ummar jihar kano zasu ji dadin gudanar da harkokin su, sannan harkokin sufuri zasu inganta Kuma za’a sami raguwar cunkuson ababen hawa a birnin Kano.

 

Yace motocin na Zamani ne kuma akwai kyakyawan tsarin da akai irin na zamani ta yadda al’umma zasu gamsu da Sabon tsarin da yasa aka samar da motocin tare da kaucewa barazanar tsaro da tafiya cikin kwanciyar hankali da lumana ba tare da cin mutunci ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...