Daga Maryam Abubakar Tukur
Tsohon mai baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin majalisar wakilai ta kasa kuma dan majalisar wakilai wanda yayi wa’adi uku, Alhaji Abdurahman Kawu Sumaila ya ce rashin daidaito daga shugabanni ne babban dalilin da ya sa kasar ke fuskantar kalubale da dama.
Alhaji Abduulrahman Kawu sumaila ya bayyana haka ne a yayin wani taron tattaunawa da kungiyar wakilan kungiyar ta Kano Correspondents Chapel Dialogue Series ta shirya a Kano.
Ya ce gazawar gwamnati wajen tabbatar da adalci ga al’umma da raba albarkatun kasa daidai, shi ne ya haifar da tashe-tashen hankula da sauran munanan laifuka da suka addabi dukkanin shiyyoyin siyasar kasar nan.
Tsohon SSA ga shugaban kasar ya kara da cewa ‘yan Najeriya sun rasa kwarin gwiwa daga gwamnati hakan ce ta sa wasu daukar makami don yin garkuwa da mutane a Arewa da tashe tashen hankula a yankin Kudu maso Gabas.

Dan takarar Sanatan Kano ta Kudu a jam’iyyar NNPP, ya ce ‘yan Najeriya ba su da tsaro a kan tituna, a gidajensu, gonakinsu, har ma a asibitoci, don haka ya kamata shugabanni su sake duba yanayinsu da salon shugabancinsu domin ciyar da Nijeriya gaba .
Kawu sumaila ya bayyana cewa idan aka zabe shi a matsayin Sanatan kano ta kudu, abubuwan da zai sa a gaba za su shafi Lafiya, Ilimi da inganta albarkatun ruwa don Kara inganta harkokin noma.
“Da a ce gwamnatocin baya sun ci gaba da karatun boko ga fulani makiyaya da gwamnatin Ibrahim Badamasi Babangida ta fara da ba’a fulani basu fada harkokin satar mutane domin neman kudin fansa da sauran miyagun laifuka ba.
“Saboda haka, ina matukar goyon bayan kafa ‘yan sandan Jihohi a matsayin wata hanya ta magance matsalolin, ta yadda jihohi za su samo mutanen Masu gaskiya da zasu taimaki wajen magance matsalolin tsaro da ake fuskanta”.
Abdurahman Kawu Sumaila, ya kuma bayyana cewa rikice-rikicen da ke faruwa a yankin Kudu maso Gabas na bukatar sabuwar hanyar da Gwamnati za ta bi domin ta zaunaws da ‘yan tada zaune tsaye domin tattauna matsalolinsu don magance su.
Sumaila wanda ke da digirin digirgir a fannin kimiyyar siyasa, ya ce zai je majalisar dattawa da dimbin gogewar domin tabbatar da adalci a tsakanin ‘yan Najeriya.