Daga Abubakar Lawan Bichi
Dan Majalisar tarraya mai wakiltar karamar hukumar Bichi Engr. Abubakar Kabir Abubakar Bichi yace bazai gajiya ba wajen baiwa harkokin ilimi kulawar data dace kasancewar Ilimi shi ne gishirin zaman duniya.
Dan majalisar ya bayyana haka ne lokaci Kaddamar da Sabbin dalibai da suka sami gurbi karatu na babba sakandire na makarantu na kimiya da fasaha na jahar kano da kuma yaye dalibai da suka Kammala karatusu a Makarantu na Kimiya da Fasaha Wanda Dan Majalisar ya dauki nauyisu.
Injiniya Abubakar yace zai cigaba da dauka nauyi karatu Yan Karamar hukumar Bichi tun daga Firamare har zuwa Jami’ar ta hannu Gidauniyarsa ta Kabiru Bichi Foundation.

Yayi Kaddamar da Sabin dalibai ko wanne zai Karbi Sabuwar Katifa, Akwatu, Liftartafe Karatu dana rubutu, Bukiti wanka, Kwando da soson wanka, Masar, Kofi da Cukali da kuma Kudin Furobishin Naira dubu Sha biyar ga kowanne dalibai.
Daya daga cikin iyaye yara Alh Lawan Ibrahim Bichi ya godewa Dan Majalisar bisa daukar nauyi Karatu Yan ‘su.
Taron ya sami halarta Yan Majalisar Jahar Mai wakitar Karamar hukumar Bichi Hon Lawan Shehu, Hon Sani Mukaddas Barde Bichi da Hajiya Yardada Mai Kano Bichi da sauran jama’a da dama.