Sarkin Kano ya yi sabbin nade-nade a fadarsa

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR ya nada Alhaji Bashir Mahe Bashir Wali a matsayin sabon walin kano da Dakta Mansur Mukhtar Adnan a matsayin sabon Sarkin Ban Kano daya daga cikin Masu zabar Sarkin Kano.

 

Anyi nadin ne a cikin fadar Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yau juma’a.

Da yake jawabi jim kadan bayan nadin, Sarkin na Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yace ya nada Dakta Mansur Mukhtar Adnan sabo da gogewar sa da irin aikace aikacan da yake gudanar a gwamnati.

 

Ya kuma hori sabin hakiman da su bayar da gudumawar da ta dace wajan munkasa rayuwar alummar masarautar Kano.

Talla

A cikin sanarwar da babban Sakataren yada labaran Masarautar kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aikowa kadaura24, yace Sabin hakiman sun nuna farin cikin su da zabin su da Mai Martaba Sarkin Kano yayi musu kuma ya nada su a matsayin hakiman da zasu bayar da gudumawa a masarautar kano.

 

Wakilin Gwamnan jihar Kano, Mataimakin gwamnan Kano Dakta Nasiru Yusif Gawuna da Ministoci da yan majalisun tarayya da na jahoji sun halarci bikin nadin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ma su shirya wa shugaban NAHCON, Farfesa Abdullah maƙarƙashiya da makircinku ba zai yi nasara ba – In ji Musa Iliyasu Kwankwaso

    Babban Daraktan kudi na hukumar raya kogunan Hadeja-Jama'are kuma...

Gwamnatin Neja za ta karya farashin kayan abinchi

Gwamnatin jihar Neja a Nigeria ta ce zata karya...

Mun kaddamar da kungiyar Tinubu Northern Youth Forum domin kare muradun Tinubu a Arewa – Alh. Auwal Ibrahim

Daga Nasiru Waziri An kaddamar da wata kungiyar matasan Arewa...

Majalisar Wakilai ta bukaci Gwamnatin tarayya ta dakatar da karin kudin kiran waya da na data

Majalisar Wakilan Najeriya ta yi kira ga Ministan Sadarwa...