NNPP ta yi kira da a hukunta Ciyaman ɗin APC da aka kama da katunan zaɓe 300 a Kano

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Jam’iyyar adawa ta NNPP da kungiyoyin farar hula, ƙarƙashin inuwar ‘Alliance for Good Governance’ sun bukaci da a gaggauta gurfanar da wani shugaba a jam’iyyar APC, Aliyu Shana da aka kama da katin zaɓe na dindindin guda 300 a Kano.

 

Shana, wanda shi ne shugaban jam’iyyar APC na unguwar Yautan Arewa, Ƙaramar Hukumar Gabasawa a jihar Kano, ya shiga hannun ƴan sanda a jiya Juma’a, tare da mika shi zuwa shelkwatar rundunar domin bincikar sa.

 

Kadaura24 ta rawaito cewa mallakar katin zabe ba bisa ka’ida kuma na ɗauke da sunan wasu ya saɓa wa sashe na 21 da 22 karamin sashe na 1 (a), (b) da (c) na dokar zaɓe ta 2022 da aka yi wa kwaskwarima.

Jarumi Ali Nuhu ya maka jaruma Hannatu Bashir a kotu bisa zargin cin zarafi

 

A wata sanarwa da shugaban NNPP na jihar, Umar Doguwa ya fitar, ya ce jam’iyyar ta umurci lauyoyin ta da su shigar da kara a kan wanda ake zargin da kuma waɗanda su ka sa shi ya aikata.

Talla

“Na umarci mai ba mu shawara kan harkokin shari’a da ya rubuta wa alkalan zabe (INEC) don bibiyar matakin da ya dace a kan lamarin,” in ji Doguwa.

 

Ya ce batun ɓoye katin zabe na PVC ya zama babban abin damuwa a Kano gabanin zaben 2023.

 

“Wannan kamen ya tabbatar da gaskiyarmu mu, za kuma mu tsaya tsayin-daka mu ga matakai na gaba da hukumar zabe mai zaman kanta da ƴan sandan Nijeriya za su dauka,” inji shi.

Da dumi-dumi: ASUU ta janye yajin aikin da ta yi watanni takwas tana yi

Jam’iyyar NNPP ta ce za ta ci gaba da bin shari’ar har zuwa tiƙewa domin kare martabar dimokuradiyya.

 

Shugaban jam’iyyar ya yaba da kokarin da rundunar ƴan sandan jihar Kano ke yi na tabbatar da gudanar da bincike mai inganci kan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Dangote ya rage farashin man fetur a Nigeria

Matatar mai ta dangote ta rage farashin man fetur...

Muna bukatar kayan aiki domin magance matsalar tsaro a karamar hukumar Nasarawa – Muhd Haruna Black

Kwamandan Jami'an sintiri na karamar hukumar Nasarawa a jihar...

Da dumi-dumi: An Sanya dokar Hana fita a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon...

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...