Hisbah ta kama mutane 31 kan zargin karuwanci da shan barasa a kazaure

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Dakarun Hukumar Hisbah a jihar Jigawa sun kama mutane 31 da su ka haɗa da mata 25 a Ƙaramar Hukumar Kazaure da ke jihar a yau Laraba, bisa zargin su da laifin aikata munanan dabi’u.

 

Kwamandan Hisbah a jihar, Ibrahim Dahiru, ya ce an kama wadanda ake zargin ne da misalin karfe 6 na safe bisa zargin karuwanci da shan barasa.

Talla

Ya shaida wa manema labarai a Dutse a yau Laraba cewa, an kama wadanda ake zargin ne a wani samame da hukumar Hisbah ta kai mai taken: “Abin da ka shuka shi za ka girba”.

 

Kwamandan ya ce an kama kwalabe 55 na barasa iri-iri da kuma lita 50 na Burukutu’ a yayin farmakin.

Talla

Ya ce an mika wadanda ake zargin da kayayyakin da aka kama ga ‘yan sanda a yankin domin ci gaba da daukar mataki.

 

Malam Dahiru ya yabawa mazauna jihar bisa goyon bayan da suke baiwa hukumar Hisbah wajen gudanar da ayyukanta.

Talla

Ya kuma bayar da tabbacin cewa Hisbah za ta ci gaba da yaki da munanan dabi’u a duk sassan jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano za ta inganta walwala ma’aikatan dake kula da harkokin kudi – Babbar Akanta

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Gwamnatin jihar Kano ta ce za...

Fadar Shugaban Kasa ta magantu kan allunan tallan Tinubu da suka mamaye Abuja da Kano

Fadar shugaban Najeriya ta nesanta kanta daga wasu allunan...

Yansanda sun kama mafarauta huɗu ƴan asalin Jihar Kano a Edo

Rundunar yansanda ta kasa reshen jihar Edo ta tabbatar...

Kotu a Amurka ta umurci FBI da hukumomin yaƙi da ƙwayoyi su saki bayanan bincike kan Tinubu

  Kotun Ƙoli ta Ƙasa ta Washington D.C. a Amurka...