Bamu taba Kai wa Gwamna Ganduje Aikin kumbotso ya Dawo Dashi ba – Garban Kauye

Date:

Daga Shazali Farawa

 

Shugaban karamar Hukumar kumbotso Hon Hassan Garban Kauye Farawa, yace Tunda aka kafa karamar Hukumar kumbotso ba’a taba samun Gwamnan Daya bata Gudunmawa kamar Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ba, musamman idan Akai la’akari da irin Ayyukan Raya kasa Daya Samar a yankin tsawon shekara Daya da Rabi, karkashin jagoranci shugaban karamar Hukumar Alhaji Hassan Garban kauye Farawa.

 

Garban Kauye ya bayyana Hakan ne, yayin da yake kaddamar da aikin hanyar Data tashi daga kan titin Zariya zuwa Cikin Garin Dan Gwauro Dake mazabar naibawa, Wanda Zai lakume kudi kusan naira miliyan 80,000.

 

” Da yake jawabi yayin kaddamar da aikin Hanyar yace, mun Samar da makarantar Yan mata amazabar naibawa a filin Cocin kwano, da Gina makarantar Islamiyya a garin Dotsa, da kujeru a Makarantun”.

Talla

“Alhaji Hassan ya Kuma Kara da bayyana gyaran Transformomi da Kuma sauran Ayyukan Raya kasa, ” wadanda Dukkansu Ayyukan ne da muka yisu cikin shekara Daya” Inji Garban Kauye.

 

Bayan kwashe shakara da shekaru al’ummar garin na Dan Gwauro, na Neman wannan hanya Basu samu ba, a Ranar Litinin Shugaban karamar Hukumar kumbotso Hassan Garban Kauye Farawa ya share musu hawaye, inda ya kaddara da aikin Kwalta Wanda zai tashi daga titin Zariya road zuwa Cikin Garin, bayan korafi da Dattawan yankin Dagatai da Kuma masu unguwanni suka Kai masa.

Talla

Haka zalika ya yabawa Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje for bisa yadda yake Baiwa karramar Hukumar kumbotso gudunwata ta hannu shugaban karamar Hukumar, sai Kuma mataimakinsa Dr Nasir Yusuf Gawuna Kuma Dan Takarar Gwamnan Kano karkashin inuwar jam’iyar APC, da mataimakinsa Alhaji Murtala Sule Garo da shugaban jam’iyar APC na jihar Kano Hon Abdullahi Abbas sunusi, bisa irin Gudunwar da suke baiwa karamar Hukumar, tare da fatan Samun Nasarar jam’iyar APC a kasa da Kano Baki Daya.

 

Taron ya samu halartar al’ummar garin na Dan Gwouro da mukarraban gwamnatin, karamar Hukumar da suka Hadar da shugaban ma’aikatan fadar Gwamnatin yankin kamalu Nasir sheka, Alh Ado malam madakin Na’ibawa da Kuma Alhaji Auwalu Zara

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Majalisar Dokokin Kano ta yi Doka kan masu tufar da yawu da majina a titi

Majalisar Dokokin jihar Kano ta amince da dokar cin...

Sanata Barau zai baiwa dalibai 1,000 tallafin karatu a Kano ta tsakiya da ta Kudu

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau...

Kamfanin Gerawa ya ba da tallafin Kwamfutoci 100 ga al’ummar Gezawa

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa   Kamfanin shinkafa na Gerawa Rice Mills...

Gwamnan Kano ya baiwa maja-baƙin Sheikh Karibullah da wasu malamai muƙami

    Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince...