Kalaman ɓatanci: Kotu ta ci Abduljabbar tarar Naira Miliyan 10

Date:

Daga Aliyu Abdullahi Fagge

 

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, a yau Litinin, ta ci tarar malamin addinin Musulunci da ake tsare, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, Naira Miliyan 10 bisa shigar da kara kan tabbatar da hakkinsa na ɗan ƙasa, inda kotun ta ce hakan rashin ɗa’a ne ga kotun.

 

Mai shari’a Emeka Nwite, a cikin hukuncin da ya yanke, ya bayar da umarnin a biya wadanda ake kara kudaden; da su ka haɗa da Kotun Shari’a ta Kofa Kudu, Kano, da gwamnatin jihar Kano a matsayin waɗanda a ke kara na daya da na biyu.

 

Mai shari’a Nwite ya kuma baiwa Kabara da lauyansa Shehu Dalhatu umarnin su biya gwamnatin jihar Naira dubu 100.

 

Talla

Alƙalin kotun ya ce da zarar kotu ta gamsu cewa an saɓawa tsare-tsaren kotu wajen shigar da ƙara, to kotu na da hakkin hukunta wanda ya shigar da karar.

 

Ya ce matakin da lauyan Kabara ya dauka na da nufin samun hukuncin da ya dace ko ta halin kaka.

 

Talla

Nwite ya ce shigar da kara a cikin wata kara mai lamba: FHC/KN/CS/185/2022 a Kano da kuma zuwa Abuja don shigar da ita dai wannan ƙarar mai lamba: FHC/ABJ/CS/1201/2022 kan wannan batu da lauyan ya yi abin alla-wadai ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu ba da umarnin mayar da Natasha bakin aikinta

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Majalisar...

Yadda Shugabanni da jagororin Jam’iyyar APC na Kano suka kauracewa tarbar Kashim Shattima yayi ziyarar ta’aziyya

Daga Fatima Mahmoud Diso   Shugabanni da jagororin jam'iyyar APC na...

Kotu ta ɗaure wani ɗan Tiktok mai wanka a tsakiyar titunan Kano

    Wata kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya...

Damuna: Mun shirya inganta wuraren tsayarwar motocinmu – Kungiyoyin Direbobin na Kano

Kungiyar matuka motocin kurkura ta jihar Kano da Kungiyar...