Daga Auwal Alhassan Kademi
Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta ce za ta tabbatar da ganin shari’a ta yi aikinta a batun kashe Ummukhulthum Sani Buhari, matashiyar da ake zargin wani dan China da aikatawa.
Dr. Abdullahi Umar Ganduje yayin wani jawabi a fadar gwamnatin jihar ya ce “Zub da jini (ne, don haka) dole maganar shari’ah ta shigo” kuma sai doka ta yi aikinta.
Ya ce tuni suka sa aka kama mutumin da ake zargi Mista Geng Quanrong, bayan mutane sun damke shi a gidansu marigayiyar ranar Juma’a.
Bayanai sun ce lamarin ya faru ne ran Juma’a da dare, inda Geng Quanrong dan shekara 47 ya kutsa kai gidansu Ummita a unguwar Kabuga cikin karamar hukumar Gwale.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike, inda ta mai da batun zuwa babban sashen binciken manyan laifuka bangaren kisan kai.