Daga Auwal Alhassan Kademi
Rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar Kano ta tabbatar da mutuwar matashiyar nan mai suna Ummukulsum Sani Mai shekaru 22 mazauniyar Janbulo dake birnin Kano .
Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu Kuma aka rabawa manema labarai a ranar Asabar.
SP Abdullahi Kiyawa ya ce sun samu kiran gaggawa a ranar juma’a 16 ga watan Satumba 2022 , da misalin karfe 9:00pm na dare daga unguwar Janbulo , Inda aka fada musu cewa wani ɗan ƙasar Chana mai suna Geng Quanrong mai shekaru 47 mazaunin Nasarawa dake Kano yaje har gidan su matashiya ya hallakata, sakamakon rashin jituwa da ta shiga tsakanin su , Inda ya yi amfani da wuƙa yaji mata munanan raunuka ɗaya a wuyan ta sauran kuma a sassan jikinta.
” Bayan samun rahotanne Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Abubakar Lawan ya tura tawagar jami’an yan sanda ƙarƙashin jagorancin Baturan yan sanda na Ɗorayi Babba SP Ibrahim Hamma, inda suka garzaya da ita asibitin Murtala Muhammad Kano wanda likita ya tabbatar da mutuwar ta shi kuma wanda ake zargin an kama shi” . Inji SP Kiyawa
Kakakin Rundunar yan sandan yace tuni Kwamishinan yan sandan jahar Kano ya bada umarnin dawo da batun babban sashin gudanar da bincike na aikata manyan laifukan kisan kai dake Bomapai domin faɗaɗa bincike. Kuma yace tuni shi Wanda ake zargi ya fara yiwa jami’an su bayanin yadda lamarin ya faru,kuma ana cigaba da bincike.