Jami’an Hisbah a Jihar Zamfara sun kama wasu mutum biyu mace da namiji waɗanda ake zarginsu da lalata a tsakiyar wata tashar mota da ke birnin Gusau na Jihar Zamfara.
Kafar watsa labarai ta PRNigeria ta ruwaito cewa waɗanda ake zargin sun yi lalatar ne tsirara ba tare da la’akari da wani na kallonsu ba.
Sakamakon haka ne jama’ar da ke tashar motar suka yi sauri suka ankarar da jami’an Hisbah waɗanda a cikin gaggawa suka isa tashar suka yi awon gaba da su.
Waɗanda suka shaida lamarin sun ce lamarin ya faru ne bayan namijin ya ƙalubalanci matar kan cewa ya fi ta rashin kunya, inda ita ma ta ƙalubalance shi, wanda daga nan suka soma wannan aika-aika.
Tuni dai aka gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban Kotun Shari’ar Musulunci ta Kankuri da ke garin Gusau.
A wani bidiyo da kadaura24 ta gani na hira da aka yi da waɗanda ake zargin, namijin da ake zargi ya ce bai san yadda aka yi hakan ta faru ba domin tun a farko ya je wurin wani biki ne inda daga nan ne yake kyautata zaton aka ba shi wani abu ya sha.
Ita kuwa macen cewa ta yi wannan abin ba halinta bane inda ta ce hasali ma sana’ar sayar da sanduna take yi.
Ta bayyana cewa idan ba ta samu cinikin sandunan bane take shiga wannan hali.