Daga Rukayya Abdullahi Maida
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta kama wata matashiya, mai suna Maryam Haruna, ƴar Shekaru 27 bisa zargin ta da watsa wa wani matashi Lawan Inuwa Ibrahim, ɗan shekaru 25 tafasasshen ruwan shayi a jikinsa.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ga manema labarai.
ya ce rundunar ta samu ƙorafi ne daga wasu mutane a unguwar Rimin Auzinawa a ranar 11 ga watan Satumba, cewa wata mata mai suna Maryam Haruna ta ƙona Lawan Inuwa Ibrahim da ruwan Shayi.
Haka kuma ya ce, “Bayan samun ƙorafin ne rundunar ta tura jami’anta ƙarƙashin Baturan yan sanda na unguwar Rijiyar Zaki CSP Usman Abdullahi inda suka garzaya da matashi asibiti tare da cafke a wadda ake zargin”.
Kadaura24 ta rawaito SP Kiyawa ya ƙara da cewa, “Bayan kai shi asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad ne likitoci suka yi masa magani a fuska da hannunsa da kuma cikinsa da ya samu ƙuna tare da kwantar da shi a asibitin.
A nata ɓangaren, wacce aka cafke ɗin ta amsa cewa ta watsa masa ruwan kuma ta yi hakan ne sakamakon rikici da ya ɓarke a tsakaninsu.
A cewar ta, tana zargin matashin da kashe mata aure ta hanyar kai tsurkun ta wajen mijinta, inda ga ƙara da cewa shi matashin ne, lokacin su na kokawa, ya yi yunƙurin watsa mata shayin.