Zamu yi amfani da Matasa a yakin neman zabe, amma ta hanyar da ta dace – Shugaban PRP na Kano

Date:

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa

 

Shugaban jam’iyyar PRP na jihar kano Engr. Abba Sule Namatazu yace jam’iyyar zata yi amfani da Matasa ta hanyar data dace a yayin yakin neman zaben shekara ta 2023.

 

“Wasu jam’iyyun suna amfani da Matasa wajen ta da tarzoma ko Basu kayan maye don su yi abubuwan da basu dace ba, don haka mu namu salon dole ya banbanta dana sauran”

 

Engr. Abba sule namatasu ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da wakilin Kadaura24 a ofishinsa dake kano.

Talla

 

Yace yana kyau matasa su gane cewa wasu yan siyasar suna amfani da su ne a lokacin siyasa, da zarar lokacin ya wuce baza su Kara ganinsu ba, ballantana su taimaka musu don gina rayuwar su ko suma sa zamo shugabannin goben da ake fada.

KARANTAKaddara ce tasa na fara rawar gala – Tahir Fagge

” Baba shakka dole matasa su shiga harkokin Siyasa Saboda sun Kashim bayan kowacce irin tafiya, Amma ya kamata matasan su rika shiga jam’iyyun da suke da kyakyawan tsarin inganta Rayuwar matasan, kamar jam’iyyar PRP da muke da tsarin baiwa matasa kulawar data dace idan Allah yasa munci zabe”. Inji Namatazu

 

Talla

Shugaban jam’iyyar PRPn yace a Irin wannan lokaci da ake shirin kada gangar siyasa, kamata yayi duk dan siyasar da ya umarci matasa su yi wani aiki wanda zai ta da hankalin al’umma to suma su nemi alfarmasa da ya Sanya ya’yansa cikin wannan aiki da yake son suyi masa.

Kungiyar Dikko Sportlight ta baiwa manajan hukumar sufuri ta jihar Katsina matsayin uban tafiyar ta

 

Eng Abba matazun yace matasa su sani suma suna da damar rike duk wani matsayi ko wane iri ne a kasar nan, matukar sun yi aiki tukuru wanda zai inganta rayuwarsu waje zama mutane na gari .

 

Shugaban jami iyar PRP yace yana fatan za’a shiga hada-hadar zabukan shekara ta 2023 lafiya tare da addu’ar Allah ya zabawa al’umma nagartattun shugabanni a kowanne matakin shugabanci a kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnan Kano ya Naɗa Ahmed Musa a Matsayin Janar Manaja na Kano Pillars

Daga Zakaria Adam Jigirya   Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Yanzu:yanzu: Gwamnan kano ya yi sabbin nade-naden mukamai

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Gwamann jihar Kano Alhaji Abba Kabir...

Yara ɗalibai na fuskatar barazanar daina zuwa Makaranta a Hotoro saboda lalacewar hanya

Daga Isa Ahmad Getso   Al'umma da Malaman makaranta a unguwar...

Kotu ba da umarnin mayar da Natasha bakin aikinta

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Majalisar...