Wata kotu a Kano ta aike da wani kansila zuwa gidan dan kande

Date:

Daga Rabi’u Usman

 

Kotun majistare mai lamba 61 dake zaman ta a unguwar mariri a kano, karkashin mai Shari’ah Salisu Idris Sallama ta aike da wani kansila zuwa gidan gyaran hali saboda kasa cika sharuddan beli.

 

Kadaura24 ta rawaito tun da fari dai an gurfanar da wani mai gida Sani dan shekara 58, guda daga cikin kansilolin Karamar hukumar kura, bisa zargin sa da laifin Zagin Cin Mutunci, bata suna, fadar magana mai fusata Mutum, da bayanan karya, harma da maganganu masu haifar da rashin zaman lafiya ga shugaban Karamar hukumar Kura Hon Mustapha Abdullahi.

Talla

 

Bayan da mai gabatar da kara a gaban kotun Barr Mahadi ya karanto kunshin tuhumar da ake yiwa mai gida sani, nan take ya musanta dukkannin laifukan da ake zargin sa dasu.

Sai da Sha’aban Sharada ya Amince da dokokin mu kafin mu bashi takarar ADP – Amb. Tasi’u Abdulrahman

Hakan ne ta baiwa Mahadi damar sake daukar wata Rana domin sake gabatar da mai gida sani gaban wannan kotu, nan take kuma kotun ta sanya ranar 22 ga watan da muke ciki domin dawowa kotun don dorawa daga inda kotun ta tsaya.

Talla

Jim kadan da fitowa daga kotun ne muka waiwaya ga lauyan da yake kare mai gida sani, Barr Yusuf Mu’az Sani tare da abokin aikin sa Barr Muhammad Aliyu Tijjani, don Neman karin bayani bisa wanda suke karewa, Barr. Yusuf yace babu abinda zaice akan wannan takaddama tsakanin Shugaban karamar Hukumar Kura Hon Mustapha Abdullahi tare da Kansila Mai gida sani.

 

Sarkin Kano ya nada Sheikh Daurawa a matsayin babban limamin jami’ar Skyline

Sai dai a karshe Kotu ta sanya me gida sani a hannun beli, mutane 2 zasu tsaya masa 1, limamin masallacin juma’a, 1, Mutum mai kamala, sannan zasu ajiye hotunan su guda 2, Dan sandan kotu zaije ya gano Gidajen su, za’a ajiye kudi a kotu naira dubu Dari biyu, a karshe kuma zasu cike takardar rantsuwa a babbar kotun jiha wadda take nuna kadarorin da suka mallaka.

Asc Musa yola Jami’in Gidan Ajiya da gyaran hali ya tisa keyar Hon Kansila mai gida sani zuwa gidan Dan kande domin Cika Umarnin kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An dakatar da Shugaba da Sakataren kungiyar APC X Eagle forum

Kwamitin zartarwa na kungiyar APC X Eagle forum ya...

Yanzu-yanzu: Naja’atu Muhd ta mayarwa da Nuhu Ribado Martani Kan barazanar da ya yi mata

Daga Isa Ahmad Getso   Yar gwagwarmayar nan Hajiya Naja'atu Muhammad...

Zargin Sharrin: Ribado ya yi barazanar maka Naja Muhammad a Kotu

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Mai baiwa shugaban kasa shawara kan...

Rusau: Kwankwaso ya bukaci gwamnan Kano ya biya diyyar mutanen da aka kashe a Rimin Zakara

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jigon jam’iyyar APC a jihar Kano,...