Daga Aminu Garba Indabawa
A kwanakin bayane Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya daga likkafar wasu daga cikin manyan masu taimakamasa izuwa mukaman mashawarta ga Gwamna din ciki harda Hon. Magaji Yau Indabawa inda ya zama mashawarci akan harkar tsare-tsare da kasafin kudi.
Anasa kokarin Hon. Indabawa ya nada mukamai daban-daban don ganin ayyukan da Gwamna Ganduje ya dora masa sun gudana yadda yakamata, daga ciki wadanda suka rabauta da mukaman akwai Hon. Aminu Isyaku Chori, Hon. Sadiq Shehu Kwasu da Hon. Umar Bala Bayero a matsayin mataimaka na musamman sai kuma Sulaiman Lawo a matsayin mataimaki.
A yayin wani gagarumin taro da aka gudanar a ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare dake sakateriyar Abdu Bako wanda ya sami halartar shugaban Karamar Hukumar birni Hon. Fa’izu Alfindiki da mataimakinsa hon Dan Bello Aminu da mataimaki ga shugaban Karamar Hukumar ta Birni irinsu
Hon. Mustapha Ali da sauran dinbin mata da matasa magoya bayan jam’iyyar APC da kuma yan’uwa da abokan arziki na wadanda suka rabauta da mukamai.
Wata kotu a Kano ta aike da wani kansila zuwa gidan dan kande
A yayin Jawabinsa Adviser Magaji Yau Indabawa ya bukacesu dasu jajirce wajen gudanar da ayyukan su, wanda hakan shima zai taimaka masa wajen sauke nauyin da gwamna Ganduje ya dora masa.
A jawani Hon. Fa’izu Alfindiki da Hon. Dan Bello Aminu Shugaban karamar hukumar birni da mataimakinsa, sun ja hankalin sababbun mataimakan na musamman da cewa an zabo sune daga dubban al’umma magoya bayan jam’iyyar ta APC dan haka kada su baiwa marada kunya.
‘Yan sanda sun kama guda cikin wadanda ake zargi da kisan dan Kabiru Gaya
Anasa bangaren daya daga cikin masu mukamin Hon. Aminu Chori ya godewa mai girma Gwamna da kuma kwamishinan ma’aikatar yada labarai Comr. Muhammad Garba da shugaba da mataimakin shugaban Karamar Hukumar birni da shi kansa Hon. Magaji Yau Indabawa bisa wannan nadi da aka yimusu inda yace babu shakka zasuyi duk iyawarsu dan ganin sun bada gudunmawarsu wajen cigaban wannan gwamnati.