‘Yan sanda sun kama guda cikin wadanda ake zargi da kisan dan Kabiru Gaya

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

 

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta tsare Abdul dan tsohon magatakardar majalisar kasar Sani Omolori da ake zargi da kashe Sadiq dan Sanatan Kano ta Kudu, Kabir Gaya.

 

Sadiq ya rasu ne a Abuja ranar Laraba.

 

Duk da cewa jama’a ba su san musabbabin mutuwarsa ba, amma iyalansa sun sanar da rasuwarsa.

 

Platinum Post ta rawaito, wani wanda ya nemi a sakaye sunansa yace ce an kashe mamakin ne ba wai mutuwa ce kawai ba, lamarin da ya sa aka fara laluben wanda ya kashe shi .

 

Talla

A cewar majiyar, dan tsohon magatakardar majalisar, wanda aboki ne marigayin, ‘yan sanda sun kama shi da laifin aikata laifin.

 

Ya kuma bayyana cewa wanda ake zargin Abdul, tare da wasu abokansa guda biyu, sun kai rahoton mutuwar Sadiq ne ga ‘yan uwansa, wadanda suka kai gawar zuwa asibiti, bisa zargin cewa ya nutse a cikin wani ruwa a wani otal dake Abuja.

 

Wani cikakken bincike da ‘yan uwan mamacin suka yi wa gawar marigayin, ya nuna wasu raunuka a jikinsa, sannan kuma kansa ya kumbura ga jini na fitowa daga lebbansa, lamarin da ya sanya ake ganin an kashe shi.

 

Talla

Cikin damuwa, yan uwan mamacin sun kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda domin a yi musu adalci.

 

‘Yan uwa sun ji ashe Abdul da abokansa ne suka kai wa Sadiq hari har suka kashe shi.

Iyalan wani mamaci sun bada gudummawar injin wankin ƙoda ga asibitin Aminu Kano

A cewar majiyar, an kama dan tsohon magatakarda ne bisa zargin kashe Sadiq Kabiru Gaya.

 

Bayan kama shi, ‘yan sanda sun binciki gidansa inda suka gano bindigar hannu, kamar yadda Platinumpost ta ruwaito.

 

Ban janye daga takarar majalisar tarayyar Gezawa da Gabasawa ba – ‘Yar takarar PDP

PlatinumPost ya ci gaba da cewa marigayi dan tsohon Gwamnan Kano yana takun-saka da dan tsohon magatakardar a kan sabani da suka samu .

 

Mai magana da yawun rundunar babban birnin tarayya, DSP Josephine Adeh, ba ta amsa kira da sakon kar ta kwana da aka aika mata ba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An dakatar da Shugaba da Sakataren kungiyar APC X Eagle forum

Kwamitin zartarwa na kungiyar APC X Eagle forum ya...

Yanzu-yanzu: Naja’atu Muhd ta mayarwa da Nuhu Ribado Martani Kan barazanar da ya yi mata

Daga Isa Ahmad Getso   Yar gwagwarmayar nan Hajiya Naja'atu Muhammad...

Zargin Sharrin: Ribado ya yi barazanar maka Naja Muhammad a Kotu

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Mai baiwa shugaban kasa shawara kan...

Rusau: Kwankwaso ya bukaci gwamnan Kano ya biya diyyar mutanen da aka kashe a Rimin Zakara

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jigon jam’iyyar APC a jihar Kano,...