Iyalan wani mamaci sun bada gudummawar injin wankin ƙoda ga asibitin Aminu Kano

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

Iyalan marigayi Justice Dahiru Mustapha sun baiwa asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano gudummawar na’urar wankin ƙoda, (dialysis machine) a matsayin sadaqatul jariya ga mahaifinsu.

Da ya ke mika na’urar ga asibitin, wakilan marigayin, Ambasada Aminu Wali, ya ce sun yanke shawarar bayar da na’urar ga asibitin koyarwa na Aminu Kano ne don bayar da gudunmawarsu wajen ci gaba da kula da lafiyar masu fama da lalurar ƙoda.
Ya ce bincike ya nuna cewa Asibitin Koyarwa na Aminu Kano ya kasance cibiyar da ta fi aikin ciwon ƙoda a fadin jihar, wadda ke aiki a kowane lokaci.
Talla
Ambasada Wali ya yi kira ga duk masu fama da ciwon ƙoda da su yi wa marigayin addu’a, haka nan kuma ya yi addu’a ga majinyatan da Nijeriya baki ɗaya.
Da yake karbar tallafin, Babban Daraktan asibitin, Farfesa Abdulrahman Abba Sheshe, ya godewa ƴan uwa da abokan arziki na marigayi Justice Dahiru Mustaph bisa hangen nesa da suka yi wajen bayar da tallafin kayan aiki da ake bukata a asibitin.
Talla
Ya kuma yi amfani da wannan damar wajen jinjinawa wadanda ke bayar da gudunmawa wajen samar da kayayyakin aiki a asibitin da ma tallafawa marasa lafiya marasa galihu da like asibitin.
Ya ce irin wadannan mutane sun hada da Alhaji (Dr) Aminu Alhassan Dantata, Alhaji A A Rano, Alhaji Garba Karfe, Injiniya Umar Ibrahim Shugaban rukunin kamfanin Aliko Oil and Gas. Sauran su ne , masu Makarantun Intercontinental Schools, da Lady Bird Schools da kuma wadanda suka nemi a sakaya sunan su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...

Mun gano yadda yan Bauchi ke mamaye dazukan Kano – Gwamnatin Kano

Daga Nazifi Dukawa     Gwamnatin jihar Kano ta ce ta gano...

Gwamnatin Kano Ta Kammala Aikin Gina Mayanka ta Naira Biliyan 1.5

Daga Zakaria Adam Jigirya     Gwamnatin jihar Kano ta karkashin Shirin...

An dakatar da Shugaba da Sakataren kungiyar APC X Eagle forum

Kwamitin zartarwa na kungiyar APC X Eagle forum ya...