Ban janye daga takarar majalisar tarayyar Gezawa da Gabasawa ba – ‘Yar takarar PDP

Date:

Daga Shehu Sulaiman Sharfadi

 

‘Yar takarar majalisar wakilan a kananan hukumomin Gabasawa da Gezawa, a jam’iyyar PDP Hajiya Amina Ibrahim B B Faruq, ta musanta rade-radin da ake yadawa cewar ta janye daga takarar da take yi.

Hajiya Amina Ibrahim B.B. faruk, ta bayyana hakan ne lokacin da take ganawa da wakilin Kadaura24 a ofishinta.
Tace yan hamayya ne suke yada jita-jitar Sabon da sun fahimci al’ummar Gezawa da Gabasawa sun karbi takarar ta hannu bibiyu sakamakon an gamsu da manufofin ta.
Talla
‘Yar takarar tace bata da niyar janyewa daga takarar da take yi, saboda ta al’umma ce Kuma Zata tabbatar ta cigaba da yada manufofin ta har lokacin da al’ummar Gezawa da Gabasawa zasu zabe ta, ta je majalisar domin kai musu aiyukan cigaba yankin.

 Hajiya Amina B B Faruq ta kuma jaddada kudirinta na ganin ta ceto al’ummar yankunan daga matsalolin dake addabarsu da suka hadar da karancin ruwan sha da zaizayar Kasa da rashin ayyukan yi ga Matasa da zarar ta samu Nasara a zaben shekara ta 2023 mai zuwa.

” Daga cikin kudurce kudurcen da nake son cimma akwai, taimakawa tsaffin ma’aikata wajen hakkokinsu na fansho da tallafawa Matasa maza da mata da inganta harkokin ilimi da lafiya da tsaro da musamman wajen Samar da ayyukan yi, Wanda suna daga cikin abubuwan da suke haifar da matsalolin rashin tsaro a fadin kasar nan”. Inji Hajiya Amina
Talla
” A zagayen mazabun da na yi na fahinci abubuwa da dama da suke bukatar kulawar gaggawa, kamar gidan ruwa na joda da aka yi shakulatin bangaro da shi, Wanda idan yana aiki sosai zai taimakawa manoman yankunan wajen yin noman rani da kuma samarwa  matane masu yawa sana’o’in dogaro da kai, yadda za su tsaya da kafafuwansu har ma su taimakawa wasu da ma samarwa musu ruwan sha tsaftatcce”. A cewar ta
Hajiya Amina B B Faruq ta koka dangane da yadda gwamnati mai ci ta Kasa aiwatar da ayyukan ci gaba a yankinsu,  kamar tituna, Samar da magudanan Ruwa a yankunan kananan hukumomin Gabasawa da Gezawa abin ya ta’azzara Wanda ya kamata a kawowa al’ummar wannan yanki dauki domin jin dadin al’amuransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...

Mun gano yadda yan Bauchi ke mamaye dazukan Kano – Gwamnatin Kano

Daga Nazifi Dukawa     Gwamnatin jihar Kano ta ce ta gano...

Gwamnatin Kano Ta Kammala Aikin Gina Mayanka ta Naira Biliyan 1.5

Daga Zakaria Adam Jigirya     Gwamnatin jihar Kano ta karkashin Shirin...

An dakatar da Shugaba da Sakataren kungiyar APC X Eagle forum

Kwamitin zartarwa na kungiyar APC X Eagle forum ya...