Da dumi-dumi: Shekara mai zuwa Inusa Yellow zai fito daga gidan yari bayan da kotun ɗaukaka ƙara ta rage shekarun da aka yanke masa

Date:

 

Kotun ɗaukaka kara ta Port Harcourt ta rage hukuncin ɗaurin shekaru 26 da wata babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Yenagoa ta jihar Bayelsa ta yanke wa Yinusa Dahiru, wanda a ka fi sani da Inusa Yellow a watan Mayun 2020.

 

Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa Mai shari’a Jane Inyang ta yanke wa Dahiru hukuncin ɗaurin shekaru 26 a gidan yari, bisa laifin safarar yara da kuma lalata da wata budurwa, Ese Oruru.

 

Dahiru, wanda bai gamsu da hukuncin ba, sai ya garzaya kotun ɗaukaka ƙara, inda ya nemi ta wanke shi.

 

Bayan sauraron lauyoyin Yellow, Abdul Mohammed, SAN, Yusuf Dankofa, Huwaila Mohammed, Sunusi Musa da Kayode Olaosebikan, kotun daukaka ƙara ta amince da daukaka karar ta wani ɓangare.

 

Kwamitin da JS Iykegh ya jagoranta, ya yi watsi da ƙarar da aka shigar kan hukuncin da aka yanke wa Dahiru kan laifukan da ake tuhumarsa da shi, sai dai ya ce kotun ƙasa ta yi kuskure da ta yanke hukuncin ɗaurin shekaru bakwai, wanda ya zarta iyakar da doka ta tanada.

 

Yayin da ta tabbatar da hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke, kotun ɗaukaka kara ta ce Dahiru zai ci gaba da hukuncin ne a lokaci guda sabanin hukuncin da kotun ta yanke a jere.

 

Bisa wannan umarni, Dahiru zai yi zaman gidan yari na shekaru bakwai daga ranar 25 ga watan Oktoba, 2018, inda zai shaƙi iskar ƴanci watan Mayun baɗi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Inganta ilimi: Jaridar New Telegraph ta Karrama Gwamnan Kano

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir...

Sanarwa ta musamman ga masu neman shiga aikin dansanda

Hukumar kula da aikin 'yan sanda na Kasa (POLICE SERVICE...

Za mu kashe Sama da Naira miliyan 105. Dan Bunkasa Harkar ilimi a karamar hukumar Dala – Hon Surajo Imam

Daga Sani Idris maiwaya   Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji Surajo...

Zaben 2027: Kwankwaso ya bugi kirji

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano, ya...