Wasu mata guda 4 sun rasu bayan kwale-kwale ya kife dasu a Jigawa

Date:

Rundunar ‘yan sandan Jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar wata yarinya ‘yar wata bakwai da wasu mata hudu bayan da kwale-kwalen su ta kife a karamar hukumar Guri.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, DSP Lawan Shiisu, shi ya tabbatar da afkuwar lamarin a Dutse babban birnin jihar.

Ya ce lamarin ya faru ne da yammacin jiya Talata, inda yarinyar da kuma matan suka shiga kwale-kwale daga Nguru a jihar Yobe zuwa kauyen Adiyani na karamar hukumar Guri na jihar ta Jigawa.

“Abin takaici, kwale-kwalen ya kife suna daf da isa inda za su je. Amma matukin kwale-kwalen ya samu damar fita da ransa, yayin da su kuma fasinjojin suka nutse,” a cewar Shiisu.

Ya ce lokacin da lamarin ya faru, direbobi da ke yankin sun yi kokarin ceto fasinjojin abin bai yu ba, sai dai gano gawarwakinsu da aka yi.

BBC Hausa ta rawaito DSP Lawan ya kara da cewa an kai gawarwakin zuwa cibiyar lafiya ta Adiyani kafin babban likitan asibitin ya tabbatar da mutuwarsu.

Mai magana da yawun ‘yan sandan ya ce dukkan matan da lamarin ya rutsa da su ‘yan kauyen ne na Adiyani, inda ya kuma ce an fara bincike domin gano abin da ya janyo kifewar kwale-kwalen.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar samarin Tijjaniyya ta yi Allah – wadai da hukuncin Kotun ECOWAS

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Kungiyar Samarin Tijjaniya ta kasa tace...

Majalisar dokokin Kano da Freedom Radio sun fara musayar kalamai

Majalisar dokokin jihar Kano ta nemi al'ummar jihar Kano...

2027: Shugabannin APC a Kano ta Kudu sun mika bukatarsu ga Sanata Kawu Sumaila

Shuwagabannin jam’iyyar APC da Sakatarorin su na mazabar Kano...

Tinubu ya sake ƙaddamar da aiki titin Abuja zuwa Kaduna

Shugaba Bola Tinubu ya kaddamar da aikin sake gina...