Daga Aisha Abubakar Mai agogo
Dakarun hukumar Hisbah a jihar Kano masu hani ga munanan aiyukan, da kuma yin nuni ga kyawawa, a Daren jiya su ka kai sumame a gidajen 3 da ake zargi, samari da yan mata kan hadu su sha shisha da sauran kayan sa maye, daga bisani su aikata masha’a.
Tun da fari, Babban kwamandan hukumar Hisbah, Dr Harun Muhammad Sani Ibn sina yace makwabtan wadan nan gidaje da ake zargi sune suka kaiwa hukumar korafi, a lokuta daban-daban, tare da nuna takaicin yadda ake barin kananan yara shiga irin wancan gida.
A lokacin sumamen an sami nasarar cafke matasa 23 maza 4 sai yan mata 19 a lokacin da suke tsaka da busa tabar shisha, inda Dakarun Hisbah ba su yi wata-wata ba su ka damko su izuwa shalkwatan hukumar Hisbah.
Bincinken da Dakarun Hisbah na farin kaya su ka gabatar, ya tabbatar da cewa ana Shan shisha da sauran kayan sa maye, baya ga aikata badala a gidan.
Wuraren da aka damko matasan sun hadar da na titin Tukur road a unguwar nasarawa, da na titin sultan road, shi ma a unguwar nasarawa, da Kuma zuwa asibitin Nasarawa wato hospital road.
A cikin wata sanarwa da jami’in yada labaran hukumar Lawan Ibrahim fagge ya aikowa kadaura24, yace Babban kwamandan hukumar Hisbah, Dr. Muhammad Sani Ibn Sina ya yi tsokaci, inda ya ba da tababbacin cigaba da kai sumame har ma da daukan matakan shari’a a kan irin wadan nan gidajen.
Sannan ya gargadi iyaye tare da Jan kunnen matasa da su guji jefa kan su cikin aiyukan masha’a domin samun shuwagabani na gari.