Daga Abdulhamid Habib Isa Tukuntawa
Daraktan Gamayyar kungiyoyin kare hakki dan Adam na kasa Kuma Shugaban Global Community for human right Karibu Yahaya lawan kabara yace kamata ya yi gwamnatin tarayya ta rushe kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASSU.
Karibu yahaya kabara ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da ya yi da wakilin Kadaura24 a Kano.
Yace yajin Aikin da kungiyar ke yi sanyawa matasa da yawa Cikin mawuyacin hali, wanda hakan ya Sanya matasan sun shiga hanyoyin da basu dace ba.

” Daga yanzu dole mu sauya akalar kiyaye-kirayen da muke, Kuma zamu matsa lambar akan dole gwamnati ta zama ko Malaman ASUU ko Kuma daliban kasar nan”. Inji Kabibu Yahaya
Yace kamata yayi gwamnatin tarayya ta ɗauki irin matakin da gwamnatin jihar Kaduna ta dauka na tilastawa malaman su koma aiki ko Kuma ta sallame su ta sake daukar wasu malaman.

” Idan gwamnatin ta ki daukar shawarar da muka bata, to su sani Matasa da yawa zasu lalace kuma kamar yadda wasu suka fara, Kuma lalacewar matasan barazana ce sosai ga Zaman Lafiyar kasar nan da ma cigabanta”. Inji Karibu Yahaya lawan
Karibullah kabara ya ce su dai Masu kare hakkin dan Adam basa goyon bayan gwamnatin tarayya ta ci gaba da lallashin Yan kungiyar ASUU ” kawai muna so a Kore su a kawo wasu ko kuma a a tilasta musu su koma bakin aiki”
Sannan yayi kira ga daliban da abun ya shafa dasu kara hakuri da halin da suka tsinci kansu a ciki ind yace komai yayi farko zaiyi karshe.