An Rantsar da Sabbin Shugabannin kungiyar yan tifa 194 dake sassan jihar kano

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

 

Wazirin Garun malam Abubakar Rabo Abdulkadir ya bukaci shugabannin kungiyar yan Tifa dake rassa daban-daban a kanan hukumomi 44 na jihar Kano, da su koyi da adalci da Jin kai gami da tallafawa marayun da iyayensu suka rasu a kungiyar cikin shugabancinsu.

 

 

Mal. Abubakar Rabo Abdulkarim ya bayyana hakan ne yayin bikin rantsar da shuwagabanni tifan na rassa daban-daban a fadin jihar kano.

 

 

Wazirin Garun Malam yace abinda suka gani na kwatanta Adalci da rainon kungiya har ta samu cigaban data samu ya isa abun alfahari a tarihi, Kuma kalubale ga sabbin d suka karbi rantsuwa a ranar Lahadi.

Talla

 

“Ganin yadda ake tafida Asusun kungiya da jagoranci na gari ya Isa abin nuni da kwaikwayo ga wadanda aka rantsar, don haka ina kira a gare ku da ku kwatanta abun da suke yi ko Kuma kwayi karko” . Mal Rabo

 

Talla

” Duk Dan Tifa yanzu zaiyi Alfahari da kungiya domin yana gani a kasa musamman a bangaren harajin da kungiya ke karba” cewar Mal. Abubakar Rabo Abdulkarim Wazirin Garun malam.

 

Anasa jawabin shugaban hadaddiyar kungiyar yan Tifa na kasa reshen jihar Kano, Kuma mataimakin shugaban Yan Tifa na kasa kwamarad Mamunu Ibrahim Takai yace, sun shirya taron ne don rantsar da shuwagabanni rassansu da ke kananan hukumomi 44 a jihar Kano.

 

Kazalika ya Kara da cewa kungiyar yan Tifa tana da tsarin zabe, Wanda duk bayan shekara hudu ake gudanarwa tun daga matakin tarayya har zuwa jihohi da kuma shiyyo-shiyyi.

 

“Tun bayan shekarar 2018 da mu kayi zaben wadanda zangon mulkinsu ya kare sai Kuma wannan shekarar da muka sake gudanar da zaben Wanda aka rantsar dasu a yau su dari da casa’in da hudu, Wanda Kuma zababbun shugabannin sune zasu shuganci duk rassanmu na fadin jihar kano”. inji Mamunu Takai.

 

Ya Kuma ja hankalin shuwagabannin rassan da su sani cewa sai Allah ya tambaye su game da shugabancin da aka basu, don haka su kare hakkin ‘ya’yan kungiyar dai-dai yadda zasu iya, su tabbatar da direbobin su na tifa sun bi doka da ka’ida, da cika mudu, don a kare hakkokin al’ummar da suke mu’amala dasu.

 

Abdulhakim Yakubu na daya daga cikin shuwagabanni tifan da aka rantsar daga shiyyar Rangaza, yayi godiya ga Allah daya nuna musu wannan Rana, sannan Kuma yace yana fatan Allah ya hada kansu ya basu iKon sauke nauyin da aka dora musu baki daya.

 

Wakiliyar kadaura 24 ta rawaito cewa Taron ya gudana a jiya Lahadi, Hudu ga watan satumbar shekarar 2022 a babbar sakatariyar kungiyar yantifa Dake unguwar kwari Na’ibawa bye pass.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An ga jinjirin watan Sallah karama a Nigeria

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad...

Yanzu-yanzu: Kasar Saudiyya ta ga watan Sallah

Daga Rahama Umar Kwaru Hukumomi a kasar Saudiyya sun tabbatar...

Tunda Musa Iliyasu Kwankwaso ya kama aiki yan APC a Kano kowa zai sha romon dimokaradiyya – Dini Falalu Fagge

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Guda cikin ya'yan jam'iyyar APC a...

Kisan Edo: Yansanda sun bayyana adadin mutanen da suka kama

Rundunar ƴansandan jihar Edo ta sanar da kama mutum...