Inganta Ilimi: Kawu Sumaila ya Baiwa Wata Yarinya Gurbin Karatu a Jami’arsa ya Al-Istigama

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

A kokarinsa na bunkasa rayuwa al’umma ta fannin ilimi, Mamallaki kuma Shugaban Kwamitin Amintattu na Jami’ar Al-istiqama, Sumaila (AUSU), Hon. Abdurrahman Sulaiman Kawu Sumaila ya baiwa wata yarinya mai  Rumasa’u Muhammad Adam gurabin karatu a jami’ar biyo bayan kwazon da ta yi a jarrabawar Waac  ta 2022.

 Rumasa’u wacce take yar asalin garin Kachako ce da ke karamar hukumar Takai a jihar Kano, ta samu kyakyawan sakamako a jarabawar Inda ta cinye kwasa-kwasai guda takwas hade da Lissafi da Ingilishi a jarrabawar watan Mayu/Yuni ta WAEC .
 A cewar sanarwar da kawu Sumailan ya sa wa hannu da kansa, wannan karimcin ya yi daidai da kokarinsa na alfahari da ilimi a cikin Al’umma ta hanyar yi wa al’umma hidima tare da cimma manyan manufofin bunkasa kyawawan dabi’u da ilimi ga dalibai a cikin jama’ar da ke kusa da wajen da kuma sauran su.
 An ba ta izinin yin karatun digiri na shekaru hudu a tsangayar koyar da ilimin kimiyya lafiya a Jami’ar AL-Istiqama, Sumaila, farawa daga shekarar karatu ta 2022/2023 .
 A lokacin da yake mika godiyarsa ga Kawu Sumaila bisa karamcin da ya yiwa yar, Hon. Hamza Safiyanu Kachako, a madadin al’ummar Takai/Kachako, ya mika godiyarsa ga Allah madaukakin sarki, ya kuma yabawa Kawu Sumaila bisa wannan karimcin.
 Daga nan sai ya bukaci wadda ta ci gajiyar da ta dauki wannan lambar yabo a matsayin kyauta ta musamman sannan ta mayar da ta saka abun da akai mata ta hanyar ninka kokarinta a lokacin da take karatu a jami’ar Al-Istiqama da ke Sumaila.
 Sannan ya umarce ta da ta zama jakadiya ta gari wadda sauran mutane da iyayenta za su yi alfahari da ita.
 “Allah ya sa wannan kokari ya zama alheri ga daukacin al’ummar musulmin duniya,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

NNPPn Kano ta bayyana matsayar Kwankwaso kan batun yi wa Tinubu mataimaki a 2027

Shugabanin bangarori biyu na jam’iyyar NNPP a jihar Kano,...

A Gaggauce: Fadar shugaban Kasa ta musanta murabus din Sakataren gwamnatin tarayya

Daga Rahama Umar Kwaru Fadar shugaban Kasa ta musanta labarin...

Gawuna ya mika ta’aziyyar rasuwar Alhaji Aminu Dantata

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna...

Nijeriya ta yi babban rashi: Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Aminu Dantata

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya...