Bayan fitar Shekarau daga NNPP, wa zai yiwa Jam’iyyar takarar Sanatan Kano ta tsakiya ?

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

A ƙarshe makon jiya ne farkon  Sanatan kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau ya aikewa da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC takardar ajiye takarar Sanatan Kano ta tsakiya da yake a jam’iyyar NNPP, gabanin ya bar jam’iyyar bisa zargin rashin adalci da yake ga jagoran jam’iyyar na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

 

Tun bayan faruwar lamarin, al’umma ke tofa albarkacin bakinsu akan wanda ya kamata ya gaji wannan takara, musamman tsohon dan takara, Aliyu Sani Madaki, wanda kwankwasiyya ta tsayar a kakar zaben shekarar 2019 da ya gabata.

 

Hal ila yau, akwai masu fatan Sanata Rufai Sani Hanga ya samu wannan tikiti, akwai masu ganin Sha’aban Ibrahim Sharada ya ajiye takararsa ta gwamna a ADP domin yazo NNPP a bashi wannan tikiti, da sauran mutane da masoya ke musu fatan alheri.

 

Bisa doka, jam’iyya na da kwanaki 14 ne daga ranar da dan takara ya tura takardar ajiye takara ga INEC, daga nan kuma sai a shirye sabon zaɓen fidda gwani, duk cikin kwanaki 14.

 

Nasara Radio ta rawaito a yanzu dai abin jira a gani, shi ne lokaci, domin bayyana wanda zai samu wannan tikiti cikin mutanen da ake yiwa zawarci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...