Daga Rukayya Abdullahi Maida
Kimanin mabiya 45 ne da suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar NNPP tare da Sanata Ibrahim Shekarau su ka yanke shawarar ci gaba da zama a jam’iyyar da nufin mara mata baya domin samun nasara a zaɓukan da ke tafe.
Da ya ke karanta sanarwar bayan taro a madadin ƴan siyasa 45 jim kadan bayan kammala taro, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Karaye/Rogo ta tarayya, Haruna Dederi, ya ce mambobi 45 da suka rattaba hannu kan takardar, sun yanke shawarar ci gaba da zama a jam’iyyar NNPP domin nuna ƴancinsu na ƴan ƙasa, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, ya jajanta wa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa
Dederi, wanda lauya ne, ya bayyana cewa, “Mun haɗa kai domin yanke shawarar ci gaba da zama a jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano tare da jajircewarmu wajen ganin jam’iyyar ta kai ga nasara a babban zabe mai zuwa. Za mu ci gaba da sadaukarwa ga babbar jam’iyyarmu don kara karfafa tushen goyon bayan ta.
“Jam’iyyar NNPP ba ta da kishiya ga duk wani mabiyin jam’iyya da jagoranci mai da ya san me ya ke yi. Wannan gaskiya ce da aka sani a ciki da wajen ƙasa . Muna kira ga daukacin al’ummarmu da su ci gaba da ba mu hadin kai domin mu karkata ga al’amuran jiharmu domin ci gaban al’ummarta tare da ceto al’ummar kasar daga halin da ake ciki na rugujewa.
“Mun amince da haƙƙin ɗan ƙasa na yin zaɓar ra’ayin sa na yin amfani da ‘yancinsa na tarayya kamar yadda kundin tsarin mulkinmu ya tanada.”