Daga Jafar Adam Jikamshi
Wani gini ya rufta kan mutane ana tsaka da kasuwanci a kasuwar wayar hannu ta Beruet dake birnin Kano.
Kadaura24 ta rawaito Wani shaidan gani da Ido Mai suna Nura Mai Mai ya shaidawa wakilmu cewa lamarin ya faru ne da misali karfe 4 saura da dai lokacin da mutane suka ta harkokinsu a kasuwar.
“ Wallahi Muna zaune kawai sai muka ji rugugu ashe ginin da yake kusa da masallacin yan izala na kasuwar, Kuma akwai mutane da yawa da Ginin ya fada kansu” inji Muhd Nura Mai Mai
Muhammad Nura ya ce shi ma Allah ne ya kiyaye shi domin bai dade da barin wajen da lamarin ya faru ba, Kuma Gini ne da ba’a dade da kammala shi ba Kuma benene Mai hawa 2.
Yanzu haka dai jami’an hukumar kashe gobara ta jihar kano ta Isa wajen domin ceto wadanda ginin a afka musu .
Duk kokarin da mukai na jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar kano ya ci tura, domin mun kirawo shi Amma wayarsa bata shiga .