Sojoji Sun Tarwatsa Yan Bindinga a Kaduna

Date:

Wata tawagar rundunar sojin Najeriya ƙarƙashin Manjo Janar Taoreed Lagbaja hadin gwiwa da wasu jami’an tsaro sun fatattaki ƴan bindiga a wasu yankunan jihar Kaduna, mai fama da ƙaruwar hare-haren ƴan bindiga.

 

Rundunar ta kai samame kan yankunan Buruku da Udawa da Manini da Birnin Gwari da Doka da Maganda da Kuyello da Dogon Dawa jiya Litinin.

Akwai yiwuwar gwamnatin tarayya zata ciyo bashin Naira Tiriliyan 11a shekara ta 2023 – Ministar Kudi

 

Yayin ɓata-kashin, sojojin sun ci ƙarfin ƴan bindigar ta hanyar amfani da manyan makamai wajen halaka ɗaya daga cikinsu, wasu uku kuma aka cafke su da ransu sai kuma wasunsu da suka tsere da raunuka.

 

Sanarwar da kakakin rundunar Kanar Onyema Nwachukwu ya fitar ta ce sojojin sun kuma gano bindiga ƙirar AK47 da alburusai da baburan hawa 18.

Ambaliyar ruwa: Gwamnatin Kano za ta rushe gine-gine da a ka yi kan hanyoyin ruwa

Rundunar sojin ta kuma nemi hadin kan al’umma wajen bankado mutanen da aka gansu da harbin bindiga tare da kjai rahoto ga hukumomin tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...