Kotun Daukaka Kara ta kori shugabannin PDP na Kano, ta tabbatar da kwamitin riko

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

A ranar Litinin ne kotun daukaka kara da ke Abuja ta yi watsi da hukuncin wata babbar kotun tarayya da ta amince da Shehu wada Sagagi a matsayin shugaban jam’iyyar PDP na Kano.

 

Shehu Sagagi, wanda tsohon gwamna Rabiu Kwankwaso ya nada a matsayin shugaban jam’iyyar a jihar kano, ana zarginsa da biyayya ga sanata Rabi’u Musa Kwankwaso wanda yanzu ya koma jam’iyyar NNPP.

 

A ranar 29 ga watan Maris ne kwamitin gudanarwa na jam’iyyar PDP na kasa, ya rusa kwamitocin gudanarwa na jam’iyyar reshen jihar Kano, da kananan hukumomi, tare da nada kwamitin riko mai mutum 6 a matsayin wanda zai maye gurbinsa.

Ambaliyar ruwa: Atiku ya bada tallafin Naira Miliyan 50 ga yan kasuwar K/ Kwari

 

A ranar 25 ga Mayu, Mai shari’a Taiwo Taiwo ya ba da umarnin Shugaban jam’iyyar PDP Shehu Sagagi ya cigaba da rike mukaminsa har zuwa karshen wa’adinsa a watan Disamba 2024.

 

Mai shari’a Taiwo ya bayyana cewa NWC ko wani kwamiti a jam’iyyar ba shi da ikon rusa shugabannin jam’iyyar na jiha da aka zaba ta hanyar zabe .

2023: Bayan ficewa daga NNPP, Shekarau ya bayyana matsayin takarar sa ta Sanata

 

Sai dai kotun daukaka kara a ranar Litinin ta yi watsi da hukuncin mai shari’a Taiwo, inda ta ce harkokin cikin gida ne na jam’iyyar, kuma jam’iyyar na da hurumin rusa shugabannin na Kano.

 

Kwamitin mutane uku karkashin jagorancin Mai shari’a Peter Ige, sun yi ittifaki kan cewa matakin da jam’iyyar PDP NWC ta dauka na rusa kwamitocin zartaswa a dukkan matakai na jam’iyyar PDP reshen jihar Kano da nada ‘yan kwamitin riko da za su jagoranci da tafiyar da harkokin jam’iyyar ba za a iya kalubalantar su ba. kamar yadda ya sabawa kundin tsarin mulkin PDP kamar yadda masu amsa na 1 – 4 suka fafata.

 

Kotun daukaka karar ta tabbatar da rushe kwamitocin zartaswa a dukkan matakai na Jam’iyyar PDP a jihar Kano da kuma nada kwamitin riko.

 

nada kwamitin ya yi daidai da tanadin sashi na 31 (2) (e) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...