Daga Auwal Alhassan Kademi
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 50 ga ‘yan kasuwar Kantin Kwari da ambaliyar ruwa ta shafa a Kano.
Kadaura24 ta ruwaito cewa an Yan kwari sun yi asarar dukiyoyi Masu tarin yawa sakamakon yadda ruwa sama ya lalata kayayyakin da darajarsu ta kai na miliyoyin sama da naira Miliyan Dubu w a karshen mako.
Atiku Abubakar, wanda tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya ne, ya bayar da tallafin ne a ranar Litinin din nan a wajen taron gagarumin karbar Sanata Ibrahim Shekarau, wanda ya koma PDP a Kano.
Atiku Abubakar ya karbi Shekarau zuwa PDP
Da yake sanar da bayar da tallafin a Atiku Abubakar ya jajanta wa ‘yan kasuwar da abin ya shafa.
“Tunaninmu da addu’o’inmu suna tare da ’yan kasuwar Kantin Kwari, Mun girgiza sosai da samu labarin bala’in da ya afka wa kasuwar ku Muna addu’ar Allah ya kare Afkuwar hakan a nan gaba.
ASUU ta Kara Tsawaita Yajin Aikin da Take yi
“Mun danu kwarai da abun da ya same ku, don haka na sanar da bayar da gudummawar Naira miliyan 50 gare ku,” in ji Atiku Abubakar.