Daga Maryam adamu Mustapha
Sarkin Kano, ya jinjinawa masu hannu da shuni da suke gina asibitoci domin tallafa wa talakawa a cikin al’umma.
Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci masu hannu da shuni a cikin al’umma da su hada karfi da karfe a fannin lafiya don inganta lafiyar al’ummar jihar kano da kasa baki daya.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran Masarautar kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aikowa kadaura24, yace Aminu Ado Bayero ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake duba sabon Asibiti mai zaman kansa da wani Dan kishin kano ya gina a birnin Kano.
2023: Bayan ficewa daga NNPP, Shekarau ya bayyana matsayin takarar sa ta Sanata
Yace ya yaba da kokarin wanda ya kirkiro asibitin na taimakawa al’ummar jihar Kano da ma kasa baki daya.
Ya kuma bada tabbacin cewa bangaren kiwon lafiya zai bada gudunmuwa domin taimakawa al’umma.
Ambaliyar ruwa: Atiku ya bada tallafin Naira Miliyan 50 ga yan kasuwar K/ Kwari
A nasa jawabin, shugaban asibitin, Dakta Muhammad Garba, ya ce ya kafa asibitin ne domin saukaka wa al’umma musamman marasa galihu.