Daga Rukayya Abdullahi Maida
Sanatan Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana matsayin takarar sa ta Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar NNPP .
Kadaura24 ta rawaito Malam Ibrahim Shekarau ya yi fice daga jam’iyyar NNPP a Litinin din nan, bayan korafin rashin Adalci da yace Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi masa .
Malam Shekarau yace ya rubutawa Hukumar zabe mai Zaman kanta ta kasa INEC ta cewa ya sauka daga takarar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar NNPP.
Ambaliyar ruwa: Atiku ya bada tallafin Naira Miliyan 50 ga yan kasuwar K/ Kwari
” Na rubutawa INEC ta kasa da ofishin ta na jihar kano cewa bana takarar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar NNPP a kai kasuwa”. Inji Shekarau
Dama dai dokar zabe ta a irin wannan lokaci tace Hukumar zabe ta INEC bata da hurumin karbar sauyin yan takara daga kowacce jam’iyya sai dai idan Dan takarar ne yace bazai yi ba, ko Kuna dan takarar ya Mutu shi ne jam’iyya zata iya sauya yan takara.
Atiku Abubakar ya karbi Shekarau zuwa PDP
Yanzu dai Jam’iyyar NNPP tana da ikon sauya sunan Malam Ibrahim Shekarau da wani Dan takarar tunda Malam Shekarau yace ba yayi .