Daga Auwal Alhassan Kademi.
Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya mika ta’aziyyarsa ga iyalai, Yan uwa, al’ummar Masarautar Funakai da na jihar Gombe gaba daya bisa rasuwar Sarkin Funakaye Alhaji Muazu Muhammed Kwairanga, wanda ya rasu a yau Lahadi 28 ga watan Agusta, 2022.
Sanarwar mai dauke da sa hannun Babban Sakataren Yada Labarai na Masarautar Kano Abubakar Balarabe Kofar Naisa ta ce Majalisar Masarautar Kano da na Jihar Kano sun kadu Sosai da samu labarin rasuwar Mai Martaba Sarkin Funakaye Alhaji Mu’azu Muhammed Kwairanga a safiyar lahadi.
Rasuwa, a cewar Sarkin Kano, ta dauke shi a lokacin da kasar nan ta fi bukatar sa, inda ya jaddada cewa, “Wannan babban rashi ne ga al’umma a fadin kasar nan da ma sauran sassan Afrika baki daya”.
2023: NNPP Zata kwace Mulki Borno daga Hannun Gwamna Zulum – Kwankwaso
Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi addu’ar Allah ya gafarta wa marigayi Alhaji Mu’azu Kwairanga na jihar Gombe, yasa kyakyawan aikin sa ya bishi ya kuma baiw al’ummar Masarautar Funakai juriyar Wannan babban rashi.