Kallon Uba Nake Yiwa Rarara, Saboda Yadda Yake Kula da ni – Abubakar Maishadda

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Fitaccen Mai shirya fina-finan nan na masana’atar Kannywood Abubakar Bashir Maishadda, wanda ya na ɗaya daga cikin furodusoahi masu tashe, ya bayyana farin cikin game da yadda shahararren mawaƙin siyasa Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara) ya ɗauke shi.

 

Maishadda ya wallafa hoton Rarara a Instagram tare da rubuta maganar da mawaƙin ke yawan faɗa masa cewa: “Malam Habu na ɗauke ka tamkar ɗan da na haifa a ciki na.”

 

Furodusan ya ci gaba da cewa, “Kullum haka ka ke faɗa min, kuma haka ka ke yi min a zahiri.”

 

Ana Neman Hana mu Damar da Kundin Tsarin Mulkin Kasa ya Bamu a Dorayi Babba dake kano – Inji Yan Shi’a

Haka kuma ya ce, “Kafin na faɗi abin da ka ke yi min, ka aurar da ni, ka ba ni jari, ka ba ni jari, ka ba ni kuɗi na yi fim, ka ba ni mota, ka ba ni mota, ka siya min mota, ka ƙaunaci dukkan ‘yan’uwa na.

 

“Wallahi tun da mu ke da kai, ban taɓa zuwa da wata damuwa ba ka yaye min ita ba.

Rundunar Sojin Nigeria ta Kori Sojojin da ake Zargi da Kisan Wani Malami a Yobe

“Allah ya saka maka da gidan Aljanna, Baba na, Dauda Kahutu Rarara. Allah ya sa ka gama da iyayen ka lafiya. Allah ya sa ka gama da duniya lafiya.”

 

Shafin fimmagazine ya rawaito Maishadda ya na yawan yin makamantan wannan tsokacin a shafin sa lokaci zuwa lokaci. Wannan alama ce ta nuna godiya da dukkan abin da Rarara ya ke yi masa, wanda in ba shi da ya ke bayyanawa ba, babu wanda ya sani

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...

Da dumi-dumi: ASUU ta sanar da ranar da zata fara yajin aiki

Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci...