Daga Auwal Alhassan Kademi
Rundunar sojin Najeriya ta kori wasu sojoji biyu bisa kisan wani malamin addinin musulunci, mai suna Sheikh Goni Aisami Gashua, a jihar Yobe.
Sojojin da aka kora sun hada da Lance Kofur John Gabriel da Lance Kofur Adamu Gideon.

Mukaddashin kwamandan da ke kula da bataliya ta 241 Reece dake Nguru a jihar Yobe, Laftanar Kanar Ibrahim Osabo, ya shaida wa manema labarai cewa kwamitin binciken hadin gwiwa da aka kafa tare da hadin gwiwar ‘yan sanda ne ya same su da laifin kisan malamin.
Kishi: Wata Mata ta Kashe Tsohon Mijinta a Jihar Kebbi
Ya ce an sallami sojojin biyu ne bisa tuhume-tuhume biyu na rashin yin ayyuka da kuma nuna kyama ga horon aikin.
Dole dan Kwangilar da ya Gina Gadar Lado ya Dawo ya gyara ta -Ministan aiyuka
Laftanar Kanar Osabo ya kara da cewa za a mika sojojin da aka kora a hannun ‘yan sanda a Damaturu domin gurfanar da su a gaban kotu.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Dungus Abdulkarim, a wata zantawa da manema labarai, yace an kama wadanda ake zargin dauke da bindigogi kirar AK-47 kuma suna hannun ‘yan sanda.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da kisan.