Atiku zai zo Kano zawarcin Malam Ibrahim Shekarau zuwa PDP

Date:

Ɗan takarar shugabancin kasa a inuwar jam’iyyar PDP ta hamayya, Atiku Abubakar na shirin kai ziyara birnin Kano a gobe Lahadi domin karbar Sanata Ibrahim Shekarau a jam’iyyarsu.

 

Ziyarar ta Atiku da wani makusancinsa ya tabbatarwa BBC na zuwa ne adaidai lokacin da ake dakon jin matsayar Sanata Shekarau da tun a makon da ya gabata ake jita-jitar zai fice daga NNPP.

 

Kishi: Wata Mata ta Kashe Tsohon Mijinta a Jihar Kebbi

A farkon wannan makon mai ƙarewa tsohon gwamnan Kano kuma Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, ya nuna alamonin raba gari da jam’iyyar NNPP.

 

Sanata Shekarau a wata hira da ya yi da BBC ya zargi jagoran jam’iyyar NNPP kuma ɗan takarar shugaban kasa, Rabi’u Musa Kwankwaso da yaudararsu.

Dole dan Kwangilar da ya Gina Gadar Lado ya Dawo ya gyara ta -Ministan aiyuka

Sannan ya shaida cewa suna kan tattauna da tuntubar juna domin sanar da matsayarsu kan ci gaba da zama a NNPP ko akasin haka.

 

Rundunar Sojin Nigeria ta Kori Sojojin da ake Zargi da Kisan Wani Malami a Yobe

Sai dai majiya mai karfi daga bangaren Atiku ta tabbatarwa da BBC cewa a gobe Lahadi Atiku zai gana da Shekarau a Kano a shirye-shiryen tabbatar da komawarsa PDP.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...

Da dumi-dumi: ASUU ta sanar da ranar da zata fara yajin aiki

Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci...